Gatanan, Gatananku.Wani yaro ne da kakarsa ke matuƙar ƙaunarsa. Da zai tafi sai ta ba shi kyautar ƙwai  ta ce masa, "Daga wannan ƙwan za ka samu dukiya mai yawa da za ka yi aure idan ka girma."

Yana fita sai ya haɗu da masu cirar kanya, sai  suka roƙe shi da ya ba su aron ƙwan, su yi amfani da shi don kaɗar kanya. Suna jefawa sai ƙwan ya fashe.

Yaro ya yi  ihu ya ce, ''La! La! La! Sai kun biya ni ƙwai na  da kakata ta ba ni domin ya zamo silar aurena.''

Sai suka ɗauki sandar da suke amfani da ita  suka ba shi. Daga nan sai ya tafi.

Daga nan, sai ya haɗu da  wasu magina. Suka buƙaci  aron sandarsa. Suka yi amfani da ita wajen gina gida.  A ƙarshe suka kakkarya sandar.

Yaron ya yi kuka ya ce, ''Kai! Kai! Kai! Sai kun biya ni sandata da  masu kaɗar kanya suka ba ni. Yayin da  suka karɓi  ƙwai na da kakata ta ba ni, domin ya zama silar aurena.''

Sai suka ba shi ciyawar  rufin ɗaki. Daga nan sai ya tafi.

Daga nan sai yaron ya haɗu da wani mai kaɗar kanya, wanda ya roƙe shi da ya ba shi ciyawarsa don ya ba shanunsa su ci.

Yaron ya yi kuku ya ce, ''Ah! Ah! Ah! Ka sani cikin damuwa. Ciyawar ba tawa ba ce, ta masu kaɗar kanya ce. Ba haka kawai maginan suka ba ni ita ba. Sun karya mini sanda, kuma ba tawa ba ce, ta makiyaya  ce. Sun bani ita ne a madadin ƙwai na. Kuma ƙwan ma ba nawa ba ne, na kakata ne da ta bani a matsayin sadakin aurena.''

Makiyayi ya ba wa yaro saniya. Yaron ya tafi da  saniya.

A hanyarsa ta komawa gida ne, yaron ya haɗu da masu bikin aure. Iyayen  amarya suka nemi ya ba su saniya. Sai ya ba su. Su kuma  suka yanka, suka cinye.

Yaro ya fashe da kuka, "Um! Um! Um! Kun sanya ni cikin matsala! Saniyar ba tawa ba ce. Ta makiyayi ce. Ya bani a madadin  ciyawata. Ciyawar ba tawa ba ce, ta magina ce. Sun bani ita saboda sandata da suka kakkarya. Sandar ma ba tawa ba ce, ta makiyaya ce da suka bani a madadin ƙwai na. Kwan ma na kakata ne, wanda ta bani domin samun sadakin aure."

Sai dangin  amaryar suka ce, ''Babu abin da za a yi sai mu biya ka. Bari mu baka amarya.'' Ya tabbata, ''Alheri danƙo ne, ba ya faɗuwa ƙasa banza.''

------------------------------------------------------------



Wani lokaci, Dan Akuya shi ne sarkin dabbobi da tsuntaye. 
  
 Sai ya kirawo su taro.

Dan Akuya ya ce musu ya yi mafarki.
  
 Duk sai suka saurara.

Ya yi mafarki a kan yunwa. 
  
 "Yaya za mu yi to?" Muzuru ta tambaya.

Kaza da Agwagwa suka ce, "Sai mu tara abinci a cikin rumbun sarki."

Sarki Dan Akuya ya ce, "A kama duk wani wanda ya ki bin doka a daure shi."

Da lokacin zaben sabon sarki ya zagayo.
  
 Sai suka zabi Muzuru.

Amma Dan Akuya ba ya son Muzuru ya zama sarki.
  
"Ni ne nan sarkin ku," Dan Akuya ya fada cikin fushi.

Dan Akuya bai dauki abinci ya kaiwa sarki ba. 
  
 Sai Saniya ta ce, "To yanzu ya zamu yi?"

Sai dabbobi da tsuntsaye su ka tattauna. 
  
 Sun yi fishi da Dan Akuya.

Sai Kare ya ce, "Koyaushe ina tare da shi lokacin da yake sarki."

Sai Tinkiya ta ce, "Ni nake saka wa 'ya'yansa kaya lokacin da yake sarki."

Alade kuwa ya koka da cewa, "Ni ne nake kula da gonarsa lokacin da yake sarki."

"Shin dan Akuya yana zaton zai ta zama a sarki ne har abada?" Tinkiya ta tambaya.

Dukkan dabbobi suka amince cewa dan akuya dole ne ya kaiwa sabon sarki abinci.
  
 Sai suka je suka same shi yana hutawa.

Dan Akuya ya ce, "Har abada ni zan cigaba da zama sarki."

"Za mu daure ka da igiya, sannan mu kai ka gaban sabon sarki."

Saniya ta jawo Dan Akuya zuwa fadar sarki. 
  
Sauran dabbobi su kai shewa.

Shi ya sa har yanzu Dan Akuya ba ya yin tafiya idan ana jan shi.

------------------------------------------------------------



A wani qauye mai suna Saye, an yi wani manomi da ake wa laqabi da Tanko, Allah ya azurta Tanko da 'ya'ya mata guda biyu, Khadija da Sadiya.

A kullum, burin Tanko 'ya'yansa su samu karatun boko mai zurfi domin taimakawa al'ummar qauyensa. amma Kash Khadija bata son zuwa makaranta, ta finson talla. Sadiya kuwa itace qarama amma tana son karatu

Kullum hankalin Sadiya yana kan zuwa makaranta. harnta kammala karatun ta na firamare da kuma makarantar gaba da firamare, sadiya ta wuce jami'a ta kammala karatun aikin likita, ta zama babbar likta a asibitin garin.

------------------------------------------------------------



Wata rana ɗan taure da ɗan damisa suka ƙulla abota.

Ana nan, sai suka tafi daji don su yi wasa.

Ɗan taure da ɗan damisa suka yi dare sosai kafin su dawo gida.

Sai ɗan taure ya ce wa innarsa, "Yau na haɗu da wani aboki mai kirki. Gobe ma za mu sake haɗuwa da shi."

Sai innarsa ta ce, "Wannan ba abokinka ba ne, yau ma na gode wa Allah da ka dawo lafiya." Don haka, kada ka je wurinsa gobe.

Shi ma ɗan damisa ya faɗa wa innarsa cewa, "Na haɗu da wani aboki mai kirki. Gobe ma zamu sake haɗuwa da shi."

Damisa ta cika da mamaki. sannan ta ce, "Dana, me ya sa ba ka cinye shi ba? idan kun haɗu gobe kar ka dawo gida sai ka cinye shi."

Washegari, sai ɗan damisa ya tafi ƙauyensu ɗan taure yana nemansa wurjanjan.

Amma ɗan taure ya laɓe a bayan innarsa. Ya ƙi fitowa daga gida.

Ɗan damisa ya taƙarƙare yana cewa, "Abokina, abokina fito mana mu yi wasa!"

Ɗan taure ya numfasa ya leƙo, sannan ya ce, "Innata ta faɗa min kai ba abokina ba ne, hanyar jirgi daban da ta mota," ni kuma ina jin maganar innata.

Don haka, jikin ɗan damisa ya yi sanyi, ya juya gida cike da takaici.

------------------------------------------------------------



Wannan shi ne Buba.

Buba yana son karatun littattafai.

Wannan saniyar sunanta Pendo.

Pendo tana son cin karas.

Buba yana  kai Pendo kiwo idan  ya dawo daga makaranta.

Ya kan shayar da Pendo ruwa a cikin tsabtattaccen kwano.

Baba kan zuba wa Pendo hatsi a daro ta ci.

Kuma yana  tatsar madarar Pendo kullum.

Pendo na samar da madara mai tarin yawa.

Baba kan kai madarar Pendo shago ya sayar.

Buba  na jin daɗin shan madara sabuwar  tatsa kullum.

Cikin murmushi, ya kan dafa  ta ya ce, "Na gode, Pendo!"

------------------------------------------------------------



Wata rana baban Aisha ya ce, "Zan miki aure."

Ta ce ba ta so, tana da wanda take so. Sai uban ya ce, "Za ki gani."

Daga nan, Aisha ta shiga damuwa. Ta faɗawa uwar, sai ta ce uban bai isa ba.

Daga nan, uban ya ce, "Ai nine babanta."

Aisha kuwa ta ce, "In Allah ya so ya yarda sai ta auri Adamu."

Sai baban ya ce, "Sai kin auri Auwal."

Daga nan, uwar Aisha ta ce, "In Allah ya yarda, kuma tana da rai, Adamu ne ɗiyar zata aura."

Sai Aisha, da murna, ta ce, "Allah ya bar mu tare. Ina son ki mama."

------------------------------------------------------------



Wata mata riƙe da ɗanta ta shiga jeji.

Ta je tsinko kayan marmari.

A jejin ta samu wata bishiya mai cike da nunannun kayan marmari.

Sai ta kwantar da yaron nan nata mai barci ta hau bishiyar.

Wani mai yaɗa zaman lafiya daga wata alƙarya ya zo wucewa ta wajen. Sai ya ga yaron. Abin ya ba shi mamaki.

Ya tambayi kansa "wai ina mahaifiyar yaron nan take?"

Sai ya tsuguna.
Кarar sarƙar da ke a wuyansa sai ta tayar da yaron.

Sai ya bar yaron ya rinƙa wasa da sarƙar.

Yana ta dariya a lokacin da yake wasa.

Matar nan sai ta duba ƙasa don ta ga wai me ke sa yaron nan dariya.

Kawai sai ta ga baƙo.

Ta yi matuƙar tsorata, hakan ya sa ta yar da jakar 'ya'yan itace.

Wannan mutumin ya kalli sama ya ce: "kar ki tsorata.

Kawai wasa nake da wannan kyakkyawan ɗan naki".

Sai matar ta sauko.

The erotot took off one of his chains. 

He gave it to the baby. "Here is a gift for you," he said.

Sai mutumin ya ce: "ki je gida da yaronki, ki ce wa mijinki ya yi ƙaura ya koma i zuwa ƙauye mafi aminci. Ɗanki ya ba ni aminci.

------------------------------------------------------------



Wata mata ta je kasuwa, ta yarda kuɗin mijinta. Matar ta damu ƙwarai.

Ta koma gida domin ta gayawa mijinta. Shi kuwa ya ce bai yarda ba

Matar ta ce "Me zai sa ba zaka yarda ba ka haƙura saboda amanar auren mu?"

Sai mijin ya ce "ba zan yarda ba, sai kin biyani kuɗi na"

"Ki je ki nemo mani kuɗi na." Ya ce mata.

Sai matar ta ce "to, kashe ni mana." Sai ya ce "zan sake ki saki uku"

"Kuma ki biyani kuɗi na." Da ta fito ƙofar gida, sai ta haɗu da wani mutun.

Ya tausaya mata, ya bata yawan kuɗin da suka ɓace. Ta yi farin ciki.

------------------------------------------------------------



Damina bata sauka ba, ƙasa ta bushe.

Biranya ta bar gida don neman ruwa da abinci.

Ta kewaye duwatsu da ƙoramai.

Sai ta zo wani wuri mai suna Tirkol.

Wannan biranyar ta yi matuƙar murna da zuwa wannan wuri.

Ta ci abinci tayi ƙiba. Amma tayi baƙin cikin rasa abokai.

Saboda haka, biranya ta yi doguwar tafiya zuwa gida.

Da ganin ta, sauran birai suka cika da farin ciki.

Suna farin ciki ta kawo masu 'ya'yan itace.

Bayan sun ƙoshi, sai biranya ta kai su zuwa Tirkol.

Sauran birai sun jin daɗin zaman Tirkol domin wadatar abinci.

Sai dai hankalin biran da suka isko Tirkol ya tashi.

Suka ce, "Baƙin biran nan zasu cinye abincin duka."

Sai biran Tirkol suka kai hari kan baƙin birai.

Suka ce, "Bakin birorin nan za su cin ye mana abinci."

Suka ce wannan gaskiya ne. Sai suka yi shawarar zama.

------------------------------------------------------------



Ina mage na?
  

  Ba gan mage na ba.
  

  Ba gan mage na ba a ko'ina
  ba.

Ina mage na?
 
Ya na qarkashi'n gado ne?
  
A'a, ya gudu daga daki.

Ina mage na?
 
 Ya na sama'n kabad ne?
  
A'a, ya na kasa'n katako na ajiya kaya.

Ina mage na?
  
Yan a Bayyan bavvan kujera ne?
  
A'a, ya na waje a cikin yadi.

Ina mage na?
  
 Ya na kusa da rumbu ne?
  
A'a, ya na yi tsalle waje taga.

Ina mage na?

  Ya na cikin Kwando ne?
  
A'a, ya na cikin aqwatin.

Ina mage na?
 
ya na waje a cikin yadi ne?
  
A'a, ya na bayyan labule.

Ina mage na?

  Ga shi nan!
  
  Ya na voye a wanan kabad!

------------------------------------------------------------



Bling ya so qwallon kafa so sai.
  
In ya na magana aka'n wasa, sai ya ce, "Qwallon kafa rai ne."

Bling ya na xaya mafi yar wasa'n koci Tsepo.
  
Koci'n murna aka'n qungiyar 'yar wasa. Mutane da yawa su'n so su shiga qungiyar.'

Wani wasa me muhimanci na zuwa.
 
 Qungiyar su'n na ta shiri ko wace rana.
  
Kowa na murna game da bavvan
  wasa'r.

Koci daga xayan qungiyar mutumin me kishi ne.
  
Ya yi kishi'n nasara'n koci Tsepo so sai.

Koci me kishi ya tafi filin da xare kafin ranar wasa'n.
  
Ya shuka abin haxari.
  
 Ya shuka umuthi!

Bling ya fara wasa'n da zafi.
  
Ya na guduwa ya ci qwallon.

Ya yar da harbi qwallo, sai ya faxi.
  
"Bling"? taron mutanen sun yi ihu.
  
 koci Tsedo ya roke. "Bling?"

"Ba a bin da zai ajiye ni a kasa!" Bling ya faxi
  
"Ma kan sa."
  
Ya tashi sama, sai ya yi wasa har qarshe.

------------------------------------------------------------



Lokacin da Binta take yarinya, mahaifiyarta na shimfiɗe ta saman wata kyakkyawar tabarma. 

Tantin Binta ta saƙa wannan tabarmar ta masumman da kaba.

Launin tabarmar ya fito sosai: Bula, ruwa hoda,  tsanwa. 

Ba tabarma ba ce kamar kowace tabarma da ke cikin ɗakinsu.

Ƙasar kewayen gidan a bushe take, ga zafi ga kuma duwatsu. 

Ana ganin kunamu da micizai wani lokaci. Binta tana kiyaye ma wannan ƙwarirrika.

Mahaifiyarta tana cewa: "Wannan tabarmar tana kare ki da miyagun abubuwa."

Binta yarinya ce mai ilimi. Ta san inda rijiya ma fi kusa take.

Kuma ta san inda garin kakarta yake. Takan je wani lokaci don ta sha nonon taguwa.

Wata rana, ba ta yi sa'a. Sai ta tafi garin kakarta,  bisan hanya sai ta ɓace cikin duwatsu. Tsoro ya kama ta.

Wata rana,  ba ta yi sa'a ba. Sai ta tafi garin kakarta,  bisan hanya sai ta ɓace cikin duwatsu. Tsoro ya kama ta.

Ga mafarkin da ta yi: Ta kwance saman tabarmarta. Kakarta ta miƙa mata nonon taguwa cikin wani kopi. Lokacin da ta miƙo hannu ta amsa sai ta farka.

Binta ta buɗe idonta a hankali. Lokacin da ta ɗaga kai,  sai ta ga wani tsuntsu bula saman wani reshe.

Da Binta ta tashi, tsuntsu ya hira ya gwada mata hanya. Binta ta bi tsuntsun.

Binta ta zo wani wuri inda hanya ta rabu biyu (2). Tsuntsun ya yadda wani guntun tabarma mai kama da tabarmar Binta.

Da ta ɗauki guntun tabarmar, Binta ta ga shaidar sawu mahaifiyarta. Can gaba kuma sai ta ga rijiyar da suke janyo ruwa.

Ƴan uwanta suna waƙa, suna rawa don sun tarbe ta. Sun yanka akuya, sun gasa don murnar ganin Binta ta komo.

Binta ta zamna saman tabarmarta kuma ta fara cin naman da aka gasa mata.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci can da ya shuɗe, dabbobi sukan yi magana. Zomo da kura sun zauna a wani wuri.

Sun yi abuta tare. Suna komi tare, har ma a wajen neman abinci.

Zomo na da wayo ƙwarai. Yana tara abinci da  yawa fiye da kura.

Ita ko wannan kura, ragguwa ce, kuma tana son cin abinci kwarai. Koda yake yanayin farautarsu ya banbanta, sun hada abincinsu tare.

Zomo yana amfani da hikimarsa wajen neman abinci da sauri. Kuma ya kan ci kafin ya kawo sauran a wurin da kura take.

A  lokacin fari, yana da wuya  su biyun su tara isasshen abinci da kansu.

Sai kura ta bar neman abinci. Ta dogara akan ɗan abinda zomo ya samo ya kawo gida. Wannan yasa zomon nan ya ji yunwa da bakin ciki. A lokacin da zomo ya dawo babu abinci, sai taji jikinta yayi sanyi.

To amma kuran nan bata nuna alamar zata canza daga halinta na dogaro akan ɗan abinda zomon nan za ya tara masu. Rayuwa ta zamo mai wuya saboda zomo baya iya ciyar da su. Don haka sai zomon nan ya kuduri ya nemo hanyar rabuwa da wanna kura.

Wata rana kura ta farka da sassafe. Sai suka fara shawarar yadda zasu rayu.

Tattaunawarsu bata kare ba saboda banbancin ra'ayoyi. Kuran nan tace bata iya samo komai saboda bata iya gudu sosai kamar zomo. Saboda haka zata zauna tayi aikin gida.

Da yamma Zomo na farauta, sai yaga danyun 'ya'yan ruman. Ya zauna dan shirya yadda zai kwashe su ya kai gida. Abin da wuya saboda gonar na da shinge.

Tare da sa himma, zomo ya kai  gabishiyar. Ya hau ya ɗebo masu yawa. Ya ci kuma ya tattara sauran ya sa a kwando, ya ɗauka. Sai yaji gajiya saboda ya cika cikinsa sosai. Sai yace bari in ɗan huta,  kawai barci ya dauke shi. Sai ga mai gona ya rutsa shi ya ɗaure shi da igiya ya tabbatar baya iya gudu.

Igiyar na da tsayi kwarai, zomo ya jata har yakai inda kura take. Yace mata akwai wata liyafa shi yasa aka ɗaure ni da igiya mai tsawo don kar in bata hanya.

Sai sakarar kurar ta kwance zomon nan ta ɗaure kanta, ta yi ta bin igiyar har ta tarad da mai gonar a fusace yana jiran isowarta yana riƙe da wata shareriyar wuƙa. Aka yanke kuranan take, aka ba karnukan mai gona suka cinye, sannan aka yi mutum-mutumi da fatar kurar.

------------------------------------------------------------



Wata rana yara uku daga Mungulu suka je farauta. Su kayi amfani da karnuka.

Lokacin da suke yawo sun ga zabi guda biyu. Suka bisu har suka kashe su.

Lokacin  tafiya gida, suna son a raba tsuntsaye. Yaro guda ya tsere da su.

Sauran yaran biyu suka bishi suka ƙwace su daga hannunsa.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci mai tsawo, an yi wata yarinya mai suna Kande. Kande yarinya ce mai surutun tsiya. Duk da cewa mahaifiyarta tana kwaɓarta a kan hakan, amma Kande ta yi kunnen uwar shegu.

Gwaggon Kande tana zaune ne a wani kwari kusa da ƙauyen su Kande. Wata rana sai ta faɗi rashin lafiya kuma babu mai jinyarta.

Mahaifiyar Kande ta yi dare wurin abinci, sai ta kira Kande ta ba ta kai wa Goggonta.

Tana cikin tafiya, sai ta ci karo da Shanshani, ba ta san Kura ce ta rikiɗe ba.

Sai Shanshani ya ce ma ta, "Me ne ne a cikin wannan  akushin?" Sai Kande ta ka da baki ta ce, "Nama ne da ƙwai da madara."

Kande ta ci gaba da cewa, "Zan kai wa Gwaggona wannan abincin ne, saboda ba ta da lafiya." Sai Shanshani ya fara tanɗar baki yana lashe-lashe  saboda ƙanshi naman dake cikin akushin Kande.

Saboda haka, sai Shanshani ya ruga a guje ya shiga gidan Gwaggon Kande.

Yana zuwa ya haɗiye ta, kuma ya ɗauki bargonta ya kwanta ya lulluɓa.

Da Kande ta iso sai ta ji gidan ya yi tsit, sai ta fara kira "Gwaggo, Gwaggo, kina ina?"

Kande ba ta ji muryar Gwaggonta ba. Sai ta shiga ɗakin da take kwance, cikin mamaki sai ta ga mutum a kwance ya lulluɓa da ƙaton bargo.

Kande ta ce, "Gwaggo ya ya kunnuwanki yau suka ƙara girma?"

Shanshani ya amsa daga cikin bargo, "Domin  inji ki sosai."

Kande ta sake cewa, "Gwaggo ya ya na ga idanun ki sun yi girma yau?

Shanshani ya amsa daga cikin bargo, "Domin in gan ki sosai."

Kande  a ƙarshe ta ce, "Gwaggo,  ya ya yau na ga bakinki ya zama ƙato?" 

Shanshani ya amsa, "Don na cinye ki." Sai ya yi tsalle daga cikin bargon ya haɗiye Kande.

Kande ta ci gaba da surutu a cikin Shanshani kuma tana yin tambayoyi iri-iri.

A qarshe, Shanshani  ya gaji da surutun Kande da tambayoyinta sai ya amayar da ita da Gwaggonta.

Mutanen ƙauyen suka rugo, kuma suka kuɓutar da Kande da Gwggonta. 

Tun daga wannan ranar, Kande ta daina surutu a wurin mutanen da ba ta sani ba.

------------------------------------------------------------



Garkar kaka tana ban shawa,  akwai dawa,  da hatsi kuma da rogo. Amma ma fi mahimmanci shine ayaba. Koda yake kaka tana da jikoki da yawa,  na sani da ni ta fi ƙwauna. Tana gayyata ta a gidanta. Tana gaya mini abubuwa da dama. Amma akwai abin ba ta gaya mini: Wurin da take nana ayaba.

Wata rana,  na ga wani babban kwando na haki ajiye cikin rana a gaban gidan kaka. Da na tambaye ta,  mine ne amfanin Kwandon, sai ta ba ni amsa kamar haka: "Kwandon mamaki ne." A kusan kwandon,  akwai ganyen ayaba da kaka take jujjuyawa lokaci suwa lokaci. Na yi mamaki. "Mine ne amfanin wannan ganyen kaka?" na tambaye ta. Sai ta ba ni amsa kamar haka: "Ganyen mamaki ne."

Akwai shawa in kana kallon kaka,  ayaba,  ganyen ayaba da kuma babban kwandon na haki. Amma kaka ta sanya ni in kiranyo ma'aifiyata don nemo wani abu. "Kaka, don Allah,  bar ni in ga abin da kike gyarawa" "Kar ki zama maras ji,  jikata,  ki yi abin aka ce ki yi" kaka take faɗi. Sai ni kuma in tafi da gudu.

Bayan na komo,  kaka tana zamne waje,  amma ba kwando,  ba ayaba. "Kaka,  ina kwando,  ina dukkan ayabar,  kuma ina" Sai ta ba ni amsa kamar haka: "Suna wani wuri na mamaki." Ban ji daɗi ba.

Bayan kwana biyu,  kaka ta aike ni cikin ɗakinta in ɗauko wata sanda da take tokarawa ta yi tafiya. Ko da na buɗe ƙofar sai ƙamshi nunannan ayaba ta tarbo ni. Tsakar ɗakin,  akwai babban Kwandon mamaki na kaka. An ɓoye shi cikin wani babban bargo. Na ɗaka shi na ji wannan ƙamshi mai daɗi.

Sai na ji muryar kaka,  na zabura,  "Mi kike yi? Ki yi maza ki kawo mini sandar." Ni kuma na yi maza na ɗauko sandar. "Mi kike ma murmushi?" in ji kaka. Tambayar tata,  ta sanya na gano da cewa,  murmushina na gano wuri mamakin da kaka take faɗi.

Washe–gari,  lokacin da kaka ta zo ta ga ma'aifiyata,  ni kuma sai na ruga gidanta don in ƙara ganin ayabar. Akwai da yawa da suka nina. Na ɗauki ɗaya na ɓoye cikin rigata. Bayan na gano kwando,  sai na laɓe bayan ɗaki na canye da sauri. Ban taɓa cin ayaba mai daɗin wannan ayabar.

Washe–gari,  lokacin da kaka take cikin garkar tana tattara kayan garka,  na sake komawa cikin ɗakin nata don in ga ayabar. Sun fara nina. Ban yi hanƙuri ba kuma na ɗauko hudu. Ina fitowa sannu sannu sai na ji kaka ta yi wani ɗan tari waje. Na ɓoye ayabar cikin riga,  kaka kuma ya wuce.

Washe-gari,  ranar kasuwa ce. Kaka ta tashi tun da safe. Kullum tana kai ayaba da rogo don ta saida a kasuwa. Ranan nan,  ban je ba na gaida kaka. Amma zan je in iske ta.

Can da maraice,  babana da kaka sun kiranyo ni. Ni san abin da na yi. Daren nan,  da na kwanta,  na yi tunanin da ba ni ƙara satar kakata ko ma'aifina ko wani can daban.

------------------------------------------------------------



Kwan, kwan!
 
 Ana buga kofa!

Alake ta cika da farin ciki.
  
 "Waye?" ta tambaya.
  
  "Mummy mun yi baki!"

"To, ina zuwa," in ji maman Alake. "Ina jin matar Malam Hassan ce, ki bude mata kofa."

Alake ta bude kofar tana murmushi. "Sannu da zuwa Mama, ki shigo ciki, mamana tana zuwa ba da jimawa ba."
  
Matar Malam Hassan ta godewa Alake.

"In kawo miki abin sha?" Alake ta tambayeta.
  
"A a, ki barshi, bana jin kishirwa, na gode," in ji matar Malam Hassan.

"Sannu da zuwa matar Malam Hassan, yi hakuri na bar ki kina jira."
  
"Babu komai kawata, Alake ta ba ni kulawa."

Maman Alake ta yi murmushi.
  
Ta ce, "Ai Alake ta iya kula da baki sosai, ina alfahari da ita."

Alake ta iya kula da baki sosai!

------------------------------------------------------------



Wata rana wani manomi ya dawo daga gona a gajiye, sai ya tambayi matarsa a bashi abincinsa, sai akace masa babu.

Sai ransa ya baci, ya yanke shawarar sakinta. da kawunsa yaji labari sai ya kirashi  yayi masa nasiha kada ya soma kodan ya'yansu.

Washe gari kawun sa yaje gidan ya yiwa matar nasiha akan idan mijinta ya dawo ta bashi hakuri.

tafiyar sa keda wuya se Manomin nan ya dawo, matarsa tai masa maraba sannan ta bashi hakuri a bisa abin da ya faru. tace masa ta gane kuskurenta

Yana fara'a yace haba komai ya wuce na yafe miki, ya ciro wasu yan kudi yace ga wannan ayi cefane harda dan tantakwashi  ki watsa mana a miya suka bushe da dariya bakidaya.

Ya fita yana daga mata hannu. yace,  "sai na dawo"

Ta tura aka yi mata cefane ta dafa musu abinci mai dadi, ta zubawa mijinta a kwanon sa ta boye sannan ta zubawa yara ma sukaci suka koshi

rayuwarsu ta koma dai-dai babu korafi babu barazana. Hakuri maganin zaman duniya.

------------------------------------------------------------



Mudi da Tanko abokan juna ne masu sha'awar guje-guje. Kullum suna guje-guje tare.

Wata rana, Tanko yace, ''Bari mu yi tsere a cikin Nahiyarmu. Bari muyi tsere domin goyon bayan haɗin kan Afirika!" "Mu tafi!" Mudi ya amsa.

Sun yanke shawarar ɗaukar fitilar haɗin kai a tafiyarsu. Sun fara tseren daga Kudu, a birnin Kef.

Daga Afirika ta Kudu sun bi ta gaɓar kogi ta yamma. Sun bi ta Kasashen Namibiya, Angola, Haɗaɗɗiyar Daular Kongo, Kongo da Kamaru. Sun huta a Abuja.

'Yan tseren Afirika ta yamma sun haɗu da abokansu na Nijeriya. Sun ci gaba tare, ta bin kogin Neja zuwa yamma.

Yanayin yashin ƙasar Mali ya basu wahalar ci gaba da tseren. Mudi shi ne gwarzo daga cikin su. Ya jagoran ce su cikin nasara.

A kogin Gini da ke Kwanakiri 'yan tseren suka wanke ƙurar da suka kwaso. Sai suka yanke shawarar tsere ta Maroko da Senegal da Mauritaniya.

A garin Kasabalanka 'yan tseren sun yi wasa da wasu matasa a gaɓar kogi. Daga nan, suka ci gaba zuwa tsallaken Afirika ta Arewa.

Tseren ya shiga ƙasashen Aljeriya da Libiya, sannan su ka tsaya a ƙasar Misira don ziyartar dala. Daga nan suka yi gaba zuwa gabas ta bin tekun Nilu zuwa Yuganda.

Sun ci gaba da tsere ta cikin Sahara da gandun dazuzzuka daban daban. An samu Karin matasa a garin Kampala. Gungun 'yan tseren sun nufi gaɓar kogin Kenya.

A garin Mumbasa sun zauna a gaɓar kogin 
inda suka ci shinkafa da Kwakwa da Kifi. 
Tanko ya ce, "Ku zo mu dauki fitilar haɗin kan Afirirka zuwa tsaunin Kilimanjaru."

Amma Tanko ya gaji. A kan hanya zuwa Tanzaniya, ya faɗi kasa. Gaba ɗaya 'yan tseren suka dakata kuma suka juya baya domin taimakawa Tanko.

Tanko ya miƙawa Mudi fitila. Ya ce, "Ka tafi da fitilar zuwa tsaunin Kilimanjaru. Ka kunna ta don haɗa kan Afirika."

Jama'a sun yi wa 'yan tseren tafi, "Ku gwaraza ne." Bayan haska fitilar haɗin kai a Kilimanjaro, sai suka juyo zuwa Afirika ta Kudu.

Sun dakata domin yin ninƙaya a tafkin Malawi. Mudi ya ce wa Tanko, "Munyi tsere tun daga Kudu zuwa Arewa sannan muka sake dawowa. Yanzu tafiyar mu ta ƙare."

A ƙarshe masu tseren haɗin kai sun dauki fitilar zuwa Kasar Zinbabuwe. 'Yan kallon sun taru a wannan muhimmin wuri. "Tanko yayi murmushi, ya ce tsere ke nan!"

------------------------------------------------------------



Can dauri, cikin garin da ake ce ma Sabuwa, an yi wani mutum da ake kiran shi Manmani, yana tare da matarshi mai sunan Rumanatu. 

Sun aifi ɗiya mata shida.

Lokacin da Rumanatu take ɗauke da cikinta na bakwai, Manmani ya ce mata. "Idan kika aifi ɗiya mace kuma, to kar ki komo gidan nan, amma in kin aifi ɗa namiji to, za ni shirya miki babbar walima!"

Lokacin da haifuwar ta zo, Rumanatu ta je wajen Fatuma. Ta tambaye ta ɗa namiji ne ko ɗiya mace ce za ta haifuwa?

Ta aifi ɗiya biyu -namiji da mace! Ta raɗama namijin sunan Hasan, ita kuma maccen Usayna. Idan ta kalli Hasan sai ta ji daɗi. 

Amma idan ta kalli Usayna, sai ranta yaɓaci. Sai ta yi tunanin, abu guda ya rage ta yi.

Rumanatu ta bar Usayna ga hannun Fatuma kuma ta kaima mijinta Hasan.

Cikin jin daɗi ta gwadawa mijinta jaririn namiji. 

Ya ji daɗi kuma ya gayyaci duk mutanen garinsu su zo wajen walimar bikin ɗanshi.

Hasan ya girma kuma ya zama kyakyawan saurayi. 

Ita ma Usayna ta girma kuma ta zama budurwa mai ɗan karen kyau.

Wata rana, Hasan yana kiyon bisasshen babanshi, sai ya hango wata budurwa mai kyau. 

"Wanan budurwar ita nike so in aura," ya faɗa.

Ko da ya tambayi aurenta sai ta fara waƙa kamar haka:
 
Mukhwana wefwe, Mukhwana. So yakhupa omunwa, Mukhwana. Nebebula omukhana, Mukhwana. Barulaka khulwanda, Mukhwana. Nebebula omusiani, Mukhwana. Barera mungo muno, Mukhwana. Iyeyi yakwa, Mukhwana. Iyindi yakwa, Mukhwana.

Kullum ana haka, ana haka. Hasan bai san abin da zai yi ba. Sai ya je wurin uwarshi, Rumanatu, ya faɗa mata. 

"Na samu wata budurwa mai kyau, kuma ina son auren ta. Amma ko da haushe na tambayeta sai ta yi ta mini waƙa."

Cikin mamaki, Rumanatu ta ce mishi, "Abin da yarinyar ta faɗa cikin waƙarta gaskiya ne. Ƙanwarka ce. Ku, tawaye ne. Babanka yana sun in aifi ɗa namiji ba ɗiya mace ɓa. Sai na bar ƙanwarka wajen Fatuma, kai kuma na kawoka gida wajen babanka."

Lokacin da Hasan ya bayyanama babanshi abin da ya faru, sai ya gane rishin gaskiyarshi. 

Ya kirayo Rumanatu kuma suka tafi tare gidan Fatuma neman Mulongo.

Lokacin da Mulongo ta dayo gida, babanta da mutanen garin sun yanka akuya don yin shagalin bikin haɗa kan Usayna da sauren ƴan uwanta bakwai maza da mata.

Bayan shekara ɗaya, Usayna ta auri ɗan wani mai kuɗin ƙauyen. 

Ta kawoma uwayenta arziki dayawa tare da jin daɗi.

------------------------------------------------------------



Fartanyar sa yar qarama ce.

Kofar dakinsa ma 'yar gajera ce.

Gadon barcinsa ma gajere ne.

Kekensa ma dan gajere ne.

Kai, wannan mutum dogo ne qwarai!

Ya maida kotar fartanyarsa mai tsawo sosai.

Kyawaren qofofin xakinsa ma ya sanya masu tsayi sosai'

Ya maida gadon barcinsa mai tsayi sosai.

Ya sayo keke mai tsawo sosai.

Ya kan  zauna a doguwar kujera. Ya ci abinci da dogon cokali mai yatsu.

A qarshe ya bar gidansa, ya koma dokar daji. Ya rayu shekaru masu yawa.

------------------------------------------------------------



A cikin daji, wata rana lokacin ana yin mugun zafi.

Ƴar Tururuwar ta yi kwanaki da kwanaki ba ta samu ruwan sha ba.

"Ina bukatar ɗashin ruwa ko da wanda ya faɗo ne daga kunnen icce."

Ba bu ko bazara.

"Idan ban sha ruwa ba za ni iya mutuwa,"  ƴar Tururuwar ta faɗa. "Ya kamata in tafi tabkin nan, da na ji labarin shi."

"Wannan tabkin yana iya tafiya da ke," wani tsofon Kurege ya yi mata kashedi.

Sai dai wannan ƴar Tururuwar ta ji ƙishirwa ƙwarai. "Idan ban sha ruwa ba za ni iya mutuwa."

Ƴar Tururuwa ta tafi neman tabkin.

Cikin ciyawa kuma ƙalƙashin reshinen itace busasu.

Har lokacin da ta ji kukan ruwan tabkin.

Ƴar Tururuwa ta ƙwalga sanyayen ruwan tabki.

Tana ta jin daɗi ba ta gani ba, ruwan tabki suna bori.

Ƴar Tururuwa ta yi, ta yi ta kama ɗan reshen iccen da yake saman ruwan. Amma ruwan sun tafi da ita.

"Ku taimake ni. Don Allah ku cece ni."

"Hawo da sauri,"  in ji Habjiya, da ta riƙe da wani reshen icce ga bakinta.



"Ba za ni tafiya ba har sai na yi ma Habjiyar nan godiya. Za ni jira har lokacin da ta dawo shan ruwa."

Tana cikin jira, wata rana sai ƴan samari biyu riƙe da kaushun harbi suka zo bakin tabkin.

"Akwai wata babbar Habjiya da take zuwa wurin ga shan ruwa," ɗaya daga cikin samarin ya faɗa. "Sai mun same ta don mu yi tuwon dare da ita."



"Ba za ni barin ƴan samarin nan ba su kashe wanan Habjiyar ba. Amma kuma ni ƙaramci ya yi mini yawa,  to yaya za ni yi?"

A wanan lokacin ne, Habjiyar ta sabko daga saman icce don ta sha ruwa.



Sai ƴar Tururuwar ta samu wata dubara.

Ta hawo saman ɗaya daga cikin samarin, ta cije shi da ƙarfi.

Ɗan sarmayin ya buga tsallo. "Wash!" yana kuwa.

Habjiyar ta ji tsoro kuma ta fira ta koma wani wuri.

Ta haka ne ƴar Tururuwa ta gode ma Habjiyar da ta cece ta.

------------------------------------------------------------



Ina son mu yi wasa da abokina Chindo.

Mun shaƙu sosai da shi, duk inda aka aike ni tare muke zuwa.

Wata rana, kakata ta aike ni shago don na sayo mata gishiri da man gyaɗa. Sai na tafi da Chindo.

A hanyarmu, sai muka ga abokanmu suna wasan ƙwallo.

"Kai! Ka ga ana wasan ƙwallon kafa!" Na ce. Ni ma ina son na yi wasan.

Sai na ce wa  Chindo, "Mu tambaye su ko za su bar mu mu yi wasan da su. Ina son wasan ƙwallon kafa sosai."

Chindo ya ce, "Mu fara zuwa shagon, sai mu dawo mu yi wasan."

Sai na ce masa, "Mu fara wasan tukunna!" "Ka san kakata ba za ta bari mu dawo ba."

Sai muka haɗu da abokan mu muka yi wasa. Ni ne mai tsaron raga. Ragar an yi ta da manyan duwatsu guda biyu.

Na yi ƙoƙari na  tsare raga ta,  saboda haka, abokaina ba su ci ko ɗaya  ba.

Mu ka yi ta wasa har sai da fili ya cika da ƙura.

Sai muka tafi shago. Ashe kuɗin aiken ya faɗi! Sai na fara kuka. Shi kuma Chindo ya ce da ƙarfi, "Ka daina kuka. Kai ka so a yi wasa tun farko."

Mu ka dawo gida ba gishiri  kuma ba man gyaɗa. Ga shi duk mun yi duƙun-duƙun cikin damuwa.

Muna isa gida, cikin fushi kaka ta ce, "Kuna ina tun-tuni?"

Sai ta yafe mana sakamakon faɗar gaskiyar da muka yi. Sannan ta gargaɗe mu ce wa, "Kada mu ƙara zuwa wasa ba da izini ba."

Mu ka bai wa agwaginmu abinci, sannan muka wanke jikinmu fes.

------------------------------------------------------------



Luwo ya tafi coci da mama'n shi.
  
Ta rike hannun shi a ka'n hanya.

A ciki coci'n aqwai mutane da yawa su'n tattara.
  
 Su na yin waka.

Luwo ya bar coci'n.
  
Mama'n shi ba ta gan shi ba.

Luwo tsaya aqa'n hanyar.
  
Ya xuba kasa'r hanya'n, sai ya yi tunani, "ina gixa
  na?"

Sai, ya bi hanyar.
  
Ya gani wani bavvan gixa.
  

  "A'a, wancan ba gida'n
  mu ba ne. gidan mu karami ne"

Luwo ya yi tafiya kax'an. Ya gan wani gixa a kan ginshiki
  
 "A'a, wancan ba gixa'n mu ba ne. Gixan mu ba ya kan ginshiki."

Ya ci gaba da tafiya. Ya gani wani karami'n gixa na bambaro.
  
 "A'a, wancan ba gida'n mu ba ne. Gidan mu na da bango'n laka."

Luwo ya kara nisa, ya gani wani karami'n gixa tare da bishiya a' waje."
  
 "A'a, wancan ba gixa'n mu ba ne. Gixan mu na da bishiya guda biyu a' waje."

A' karshe Luwo ya gan Mamma'n shi ta na zuwa gareshi. Luwo gudu waje'n ta.
  
Maman shi ta ce, "mu je gixa!"

Wanne ne gixan Luwo?

------------------------------------------------------------



Ada tayi dariya da jin tatsuniya mai ban dariya.
  
Ta na murmushi.

Mai ada take ji?

Gisa na fushi.
  
Ya turbune fuskan
  sa.
  
Mai ya bashi haushi?

Yuadoo na tsoron duhu.
  
Kowa na jin tsoro wani lokaci.
  
Amma, Yuadoo na iya neman taimako.

Chidubem ya damu da aikin makarantar sa.
  
Zai iya gayawa malamin sa.
  
Zai iya neman taimako.

Lushan na wasa!
  
Ba laifi bane ka zama wawa wani lokaci.

Eruro na bakin ciki.
  
Yanayi kan zo ya tafi

Ayator na cike da farin ciki.
  
yana cikin murna.
  
Yanayi kan zo ya tafi.

Hadiza na kewa.
  
Ya kamata ta nemi abun yi.

Ayo na fushi.
  
Yana cikin takaici.
  
Fushi abu ne mara daxi.

Labake na farin ciki.
  
Mai dalilin farin cikin ta?
  
Mama ta yi abincin da tafi sha'awa.

Zege yaji barci.
  
Ya gaji sosai.
  
"Amma dakata, barci yanayi ne?" Efe ya tambaya.

Efe ya rikice.
  
Ka na iya ba shi amsa?

Tega yana jin mamaki da kaxuwa.
  
Ya ji wata gulma.
  
Gaskiya ne?

Yebo ba shi da lafiya.
  
Tana jin takaici.
  
Tana bukatan magani da hutawa domin samun sauki.

Sekyen na gamsuwa.
  
Ta gama aikace-aikacen gida.
  
Yanzu ta na iya wasa.

Vandefan bai da aikace-aikacen gida yau.
  
Ya nuna wa Sekyen manyan yatsun sa biyu.
  
"Yawwa, yanzu muyi wasa! ya ce.

------------------------------------------------------------



Ina ƙaunar malamata.

Malama ce mai  ƙwazo.Tana da kirki da haƙuri.

Ta yi kitso mai kyau a kanta.

Ta sa duwatsun kitso masu launi a gashinta.

Duwatsun kitson nata sun ƙunshi tsanwa, fari, ja da rawaya.

Inna, don Allah zaki yi min kitso irin na malamata?

Ni ma idan na girma zan sa duwatsun kitso a gashina.

Nima zan girma in zama kamar malamata!

------------------------------------------------------------



A wata shekara lokacin bazara ya yi tsaho sosai. Dan haka dukkan koguna suka kafe, sai kogin baiwa ne kadai bai kafe ba.
  
 Dukkan dabbobi suna matukar jin kishirwa, dan haka suka kira taro a tsakaninsu.

Rakumi shi ne ya fara magana ya ce, "To kun san dai cewa dukkaninmu muna matukar jin kishirwa, sannan kuma dukkan koguna sun kafe, sai dai Kogin Baiwa shi kuma yana da nisa sosai. Yanzu ya ya za mu yi?"

Sai doki ya ba da shawara cewa, "Wasu daga cikinmu mu tafi Kogin Baiwa, mu sha ruwa sannan mu debo mu kawo wa sauran su sha."

Saniya ta ce, "Gaskiya wajen da nisa sosai, idan muka
tafi wadanda muka bari za su mutu kafin mu dawo."

Sai Tinkiya ta ce, "Maaa Maaa! Ni dai zan je Kogin Baiwa na sha ruwa."
 
Sai Akuya ma ta ce, "Meee Meee! Nima zan je Kogin Baiwa."
  
Sai Kaza ta ce, "Keee keee keee! Nima dai zan je Kogin Baiwa."

Dukkan dabbobin suna so su je, dan haka Rakumi ya jagorance su suka kama hanya.

Wannan tafiya ba mai sauki ba ce, Zabo shi ne a can baya. "Abokaina ni fa na gaji da tafiya, ba zan iya zuwa Kogin Baiwa ba," Zabo ya ce.
  
Sai Kaza ta hadiye Zabo.

Suka ci gaba da tafiya. Sai Kaza ta ce, "Gaskiya na gaji, na hakura ba na so na je Kogin Baiwa."
  
 Sai Tinkiya ta hadiye Kaza.

Suna cikin tafiya sai Tinkiya ita ma ta gaji.
  
Sai ta ce, "Nima na gaji ba na bukatar zuwa Kogin Baiwa sam."
  
Sai Akuya ta hadiye Tinkiya.

A na cikin tafiya, Akuya ita ma ta gaza, domin ba za ta iy  cigaba da tafiyar ba. Sai Doki ya juya ya hadiye Akuya.
  
Lokacin da Doki ya gaji da tafiya, sai Saniya ta juya ta hadiye shi.

Da Saniya ta gaza, sai Rakumi ya juya ya hadiye ta.

Da Rakumi ya ga shi kadai ya rage, sai ya yi iya kokarinsa domin ya isa Kogin Baiwa.
  
A karshe Rakumi ya isa Kogin Baiwa a gajiye bayan ya sha wahala.

Daga zuwa sai Rakumi ya kwanta ya amayo Saniya.
  
Ita kuma Saniya ta amayo Doki, shi kuma Doki ya amayo Akuya.
  
Ita kuma Akuya ta amayo Tinkiya, ita kuma Tinkiya ta amayo Kaza, ita kuma Kaza ta amayo Zabo.

Ta haka dukkan dabbobin suka samu dama suka sha ruwa a Kogin Baiwa.

------------------------------------------------------------



Baba da inna suka tafi gona suka bar jaririnsu a wajen yayyensa.

Sai yaran su kai ta wasa har suka manta da jaririn.

Sai ga balbelu sun zo wucewa, suka ji jariri yana ta kuka.

Sai suka dauke jaririn daga cikin bargonsa suka tafi da shi.

Sai inna ta hango balbelu suna tafiya da jaririnta a sararin samaniya.

Balbelun su kai ta kula da jaririn yadda ya kamata.

Watarana balbelu suka fita yawo, sai kwado ya zo ya hadiye jaririn!

Bayan kwanaki uku sai kwado ya dawo da jariri waje iyayensa.

------------------------------------------------------------



Yan'uwa uku Udoo, Erdoo da Eryum, suna sauraran yadda rowan sama ke sauti (da yake sauka), suna kuma son rawa a ciki, su kuma tava bakangizon da ya bayyana a sararin sama. Mama ta ce "A'a."

Suka yi kuka, da fatan zata canja ra'ayinta, amma hakan bai yi amfana ba. Har ma Eryum yayi qoqarin sulalewa ya fita gidan domin ya ga bakangizon.

Mama ta kama shi kafin ya fita. Tayi magana da murya mai ƙarfi saboda Eryum da 'yan'uwan sa mata suma su ji.

"Zaku iya kama mura," ta ce. "Gashi baku son ferfesu kuma dole ne ku sha in har mura ta kamaku," ta yi murmushi.

Da fatan za su ce ta ba su tatsuniya, sai ta ce, "Bakangizo, rafi ne mai sihiri da ke da ikon warkarwa," amma yana can cikin sararin sama yadda baza ku iya taɓawa ba. Idan mura ta kamaku, bakangizo ba zai iya taimakon ku ba.

Yaran suka yi tunanin wannan maganar.

"Mama don Allah ki ba mu tatsuniyar mu ta bakangizo," Erdoo ta ce. "I, don Allah mama ni ma ina so in ji," Udoo ma ta sa baki. "Nima haka," Eryum  ya roƙa, tare da ɗaga ƙananan yatsu uku sama.

Da wasa ta ce, "Bari mu gani mmmmm! Toh, ku matso kusa, ga mama mai ba da tatsuniya nan!"

Erdoo ta ruga da gudu ta ɗauko muciyan da suke amfani da ita mai nuna alamar izini. Da ta ɗauko, sai ta miƙawa Mama. Sai Eryum ya ɗauko ɗankwalin da Mama za ta ɗaura. Wannan bai taɓa fasa bata sifan mai tastuniya ba. 

Sai suka zauna shuru don suji wannan tastuniyar da suka riga suka ji saudayawa. Udoo ta hura usir mai cewa  Mama ta fara, sai tastuniya ta soma.

"Da can, bakangizo rafi ne mai sihiri. An ɓoye shi ne cikin dazuzzuka mai launin kore a garin Mbadede. Saboda yana da ikon warkarwa saboda, ana tsaron rafin."

Idan kuna ciwo, sai ku sha ruwan. Bakagizon na farin ciki a kullum ya raba ruwan da masu buƙata. Amma fa, ba ya son mutane mara sa kirki.

"Saboda  sihirin rafin, ana samun madara mai sanyi a bakin rafin. Duk wanda ya zo shan ruwan rafin,  ya kan more wannan madara mai sanyi ɗin, musamman ma yara.

Wannan madara mai sanyi ɗin daga rafin na da launuka kamar  ja, ruwan lemo, ruwan ɗoruwa, kore, shudi, lilak, da ruwa mai haɗin shuɗi."

"Wata rana, wata gagararriyar tsohuwa mai suna Mbom tazo daga wata ƙasa mai nisa. Da shigar ta garin, sai ta haɗu da wani maitsaro. Bai san ta ba kuma sai ya ji wani iri a jikin sa game da tsohuwar. Amma bai mai da hankali ga yanayin da ya ji game da ita ba.

Sai ya nuna mata hanyar zuwa rafin sannan yace da ita ta girmama rafin. Mbom ta amince sai ta wuce zuwa rafin."

"Da ta sha ruwan, sai ta warke. Sai ta waiwaya ta tabbatar babu mai ganin ta.

Mbom ta ɗauki dutse ta jefa cikin rafin. Sai ta ga yadda ruwan  ya yi sama ya kuma warwatsu yana bi koina. Sai ta ji daɗi, ta ɗauki sandan itace ta jefa ciki, ruwan ya sake yin yadda yayi da farko."

"Mbom ta yi tsalle ta faɗa cikin rafin da fatan ta sami rai dawwamamme. Tana faɗawa cikin rafin, sai ruwan ya taso sama. Ya cigaba da hawa can sama yadda ba zai sake dawowa garin Mbadede ba. Amma, wasu lokuta, bakangizon na bayyana ne bayan ruwan sama domin ya sake ji kamar rafi.

"Kurungus. Karshen tatsuniya ta ke nan," Mama ta ce.

"Toh kaunatattuna, ku faɗa min dalilin da yasa kuke son wannan tatsuniyar sosai? Mama ta tambaya. "Sau da dama kukan ce in baku wannan tatsuniyar."

"Ina son ta ne saboda tana tuna min da in yi la'akari da yadda nake ji game da mutane," Udoo ta ce tana murmushi.

"Tana tuna min da launukan da bakangizo ke da shi." Erdoo ta kara.

Eryum ma yayi ƙoƙarin faɗin nasa ra'ayin da fatan zai yi dace, "Ina son tatsuniyar ne domin tana tuna min da madara mai sanyi! Za'a iya bani yanzu, don Allah?"

"Mmmmm. Akwai sanyi yanzu, bari mu sha madara mai sanyi gobe ko?" Mama ta ce. "Sai ta sake cewa wata rana, zan baku tatsuniyar yadda ƙarshen Bakangizo ta kasance."

------------------------------------------------------------



Ina son yin karatu.

Wa zan karatawa?

Ƙanwata ta yi barci.

Wa zan karantawa?

Mahaifiyata da kakata suna hidima.

Wa zan karantawa?

Mahaifina da kakana suna hidima.

Wa zan karantawa? Zan karantawa kaina.

------------------------------------------------------------



A da can anyi wani gari mai suna Jummo wanda ke da mutane masu ɗinbin yawa.

Kash! sai dai garin basu da ilimi. Wannan ya sa duk sun fi son noma.

Amma a garin akwai wani yaro mai suna Barau wanda shi kaɗai ke karatu.

Abokansa na ta yi masa dariya. Bayan yagama karatu sai ya tafi birni.

Sai ga Barau ya dawo da motoci da kuɗi ya ba iyayensa da yan garinsu.

Ya ce musu ilmi jarine, kowa ya ɗauko ɗansa ya sa shi a makaranta.

------------------------------------------------------------



Za'a yi mata auren dole amma bata so. Babanta kuwa ya ce "sai an yi."

Ita ba ta so domin tana da wanda take so amma aka ce sai anyi.

Ita ta ce ba ta so ta kuma fada wa mamanta.

Ko da yake uban ya gane ba ta son Auwal, uban dai ya nace shi zai ba ta!

Maman ita kwa ba ta son Auwal, don tana goyon bayan yar ta.

Baba ya ce jibi za'a yi auren, sai ta ce ba zai yuwu ba. Ya ce "za ki gani"

Ta ce "na ga alkairin ka, na ga sharri."

Da uwar ta ga maigidan ya nace, sai ta yi wa yar albishir zata ba ta Adam

Sai yar ta ce "mama, ina son ki. Allah ya bar mu lafiya."

------------------------------------------------------------



Damisa koda yaushe tana qoqarin kama barewa.

Barewa kullum na kuɓuta daga tarkon damisa.

Wata rana, Damisa ta kira Barewa, ''Zo mu zama abokai. Abun da kike ci, ni  bana ci. Babu dalilin yin gaba.''

Barewa ta amince. Sai damisa ta ce, ''Mu yi rantsuwa don zama abokai. Idan ɗayanmu ya saɓa alƙawari zai mutu.''

Suka yi rantsuwa ta zama abokai. Barewa ta kwanta ƙarƙashin bishiya, damisa kuma a kan rassan bishiya.

Jim kaɗan barewa ta yi ƙiba, damisa kuwa ta rame.

Damisa ta yi kwaɗayin cinye barewa. Don saɓa rantsuwa da  tunanin  bata da ɗa.

Damisa ta yi tsalle domin kama Barewa. Sai ta maƙale a tsakanin rassa biyu.

Barewa ta tsorata. Ta buga tsalle tana kuka, ''ɓeh! ɓeh!''

Damisa ta yi roƙon cewa, ''Ƙawata, taimaka mini. Mun yi rantsuwa kan duk wanda ya karya alƙawari zai rasa ɗa.''

Barewa ta amsa, ''Iyayenki ne suka yi rantsuwa.'' Yanzu matsalar ki ce.

------------------------------------------------------------



Abebe ya fara zuwa makarantar boko. Wannan ita ce shekararsa ta farko a makaranta.

Babansa manomi ne. Wata shekara baban Abebe ya shuka shinkafa a gonarsa. 
  
Kowacce rana bayan an tashi daga makaranta, sai Abebe ya tafi gona domin ya taimaki babansa.

A gefen gonar su Abebe, akwai filin kwallo. Wani lokaci da yamma Abebe yana wasa da tsuntsaye, sai ga yaran turawa guda hudu sun zo za su yi wasan kwallo. 
  
Yaran suka fara wasa. Kwallo tai tsalle ta fada cikin gonar shinkafa.

Kwallon ta bata shukar su Abebe. Daya daga cikin yaran ya ruga ya shiga cikin gonar shinkafa domin ya dauko kwallonsa, sai ya tattaka shukar shinkafar!
  
Daga nan yaran suka cigaba da wasansu. Kwallon kuma tai ta tsalle tana fadawa cikin gonar shinkafa.

Yaran kuma su ka yi ta tattaka shukar shinkafar domin su dauko kwallonsu. A duk lokacin da suka shiga, sai sun lalata wani bangare na shukar shinkafa.
   
Abebe da babansa ransu ya baci saboda lalacewar shukarsu.

Da Abebe da babansa babu wanda yake jin turanci. Ba su san yadda za su gaya wa yaran turawa su daina shiga cikin gonar suna bata musu shuka ba.
  
Su kuma yaran turawan ba sa jin kowanne yare sai turanci.

Baban Abebe ya ce, "Dana ka yi amfani da abin da ka koya a makaranta mana, ka gaya musu su daina jefa kwallo cikin gonarmu!"
  
Amma a wannan lokaci, Abebe bai iya komai ba sai haruffan A, B, C, D, E, F.

Abebe yana son ya yiwa yaran tsawa domin ya dakatar da su, amma bai san yadda zai musu magana da turanci ba.

Haka kwallon nan ta cigaba da tsalle a cikin gonar su Abebe. Daya daga cikin yaran ya rugo da gudu cikin gonar.

Abebe ya ruga da gudu wajen yaron yana daga masa hannuwansa. Ya fara yi masa tsawa iya karfinsa ya ce, "A, B, C, D, E, F!"

Ya kara buga musu tsawa har sau uku ya ce, "A, B, C, D, E, F!"

Baturen yaron ya tsaya da gudun da yake yi a cikin gonar. Abokansa su ma suka tsaya cak suna kallon Abebe.
  
Sai yaran suka yi magana da junansu da turanci suka yi murmushi. Domin sun fahimci abin da Abebe yake kokarin sanar da su.

Yaron dake rike da kwallon ya taka a hankali ya fita daga cikin gonar.
  
Sai yaran turawan su hudu suka tafi nesa da gonar su Abebe suka cigaba da wasansu.
  
Baban Abebe ya yi mamaki sosai. Ya gamsu cewa lallai dansa yana jin turanci.

Ya ce, "Lallai dana kana da kokari da fahimta!" Sai ya yi alfahari da dansa.

Abebe ma kansa ya yi mamaki kuma ya ji dadi. Har ma ya rasa abin da zai ce.

Baban Abebe ya cigaba da karfafa masa gwiwa a kan ya kara kokari a makaranta, domin ya cigaba da karatunsa idan ya kammala makaranta.

------------------------------------------------------------



Launi bakwai a cikin bakan-gizo.

1. Launin ja.

Ya sanya jan riga.

2. Launin ruwan goro.

Wane launi ne na ruwan goro a wannan hoton?

3. Launin ɗorawa.

Wane ne launin ɗorawa a wannan hoton?

4. Launin kore.

Wane ne launin kore a cikin wannan hoton?

5. Launin shuɗi.

Wane ne launin shuɗi a cikin wannan hoton?

Launin kunkumadi.

Wane ne launin kunkumadi a wannan hoton?

Launin shan-shan bale

Launin  Shan-shan bale ya fi dacewa. Wene launin ka keso?

Waɗanne ne launuka bakwai na Bakan-gizo?

------------------------------------------------------------



Da dodona,  muna kallon tsuntsaye a sama.

Da tsuntsayena,  muna ganin baƙin biri cikin icce.

Da ni da baƙin birina,  muna wasa saman tudu da raƙumman daji.

Tare da raƙummana,  muna ƙera ƙwallon laka tare da birina.

Kullum,  tare da birina,  muna cin ayaba tare da baƙin biri.

Baƙin biri da biri suna tsoron kunkuru.

Da kunkuruna,  muna komawa gida lafiya da miciji.

Da micijina,  muna waƙa da bushe-bushe kusan tabki.

Iyalina gaba ɗaya muna rayuwa mai daɗi.

------------------------------------------------------------



Wata rana, na ga babbar mota tana tafiya a kan titi.

Ita kuma ƙaramar mota tana tahowa a kan titi.

Matuƙin babbar mota yana magana da wayar hannu.

Ba ya kallon gabansa.

Kash! Sai aka samu babban haɗari.

Sai motar 'yan agajin gaggawa da 'yansanda suka kawo ɗauki.

Daga baya, motoci masu ƙugiya guda biyu suka zo, suka janje motocin.

Na razana matuƙa.

------------------------------------------------------------



Wata rana mai akuya ya tafi kasuwa, ya bar akuyar da yunwa

Sai akuyar ta tafi gonar wani mutum ta yi ɓarna

Da mutumin ya ganta, sai ya kawo ƙarar ta gurin mai  ita.

Nan, mai akuyar ya ce "ba ruwana."

Mai gona ya ce "haka kacce?"

Mai gona ya tafyarsa. Da gari ya waye sai akuyar ta koma gonar

Sai mai gonar ya kameta. Akuya bata dawo gida ba.

Mai akuya ya damu sosai!

------------------------------------------------------------



Watanni da dama, sararin samaniya ya kasance a bushe. Alaramma, babban malamin gari, ya yi magana da maigari kan ayi adduar roƙon ruwa. Jama'a suka taru a ƙofar gidansa, saboda sun ƙagara a sami saukar ruwan sama.

Lokacin da ya fito, sai ya tabbatarwa da jama'a cewa Allah zai  bada ruwa ba da daɗewa ba in an yi addua, domin su sami damar yin shuka.

Yara na wasa a waje lokacin da muke tsammanin saukar ruwan sama. Bayan jimawa kaɗan, sai muka ga farin gajimari ya taso daga can gabas. Da alamu hadarin nan zai yi ruwa.

Mutane na ta tunanin abin da zai kasance. Mahaifiyarmu ta ƙwalla mana kira daga cikin ɗaki, "Kai! Ga hadari nan ya yi baƙiƙirin, ku shigo ciki."

Sai kawai aka fara ruwa.

Da farko muna ta murna da saukarsa. Amma sai ya ƙi tsayawa.

Sakamakon anbaliyar ruwa,sai gadar da ta haɗa mu da birni ta karye.

Gidajenmu suka rurrushe. Alheri ya so ya zamo annoba.

Kowa ya yi shirin shuka, amma yanzu ba dama. Mutanen ƙauyenmu sun so saukar ruwan sama matuƙa; amma yanzu ba sa buƙatarsa ko kaɗan. Mun rasa gadarmu da gidajenmu.

Sai ga wata sabuwar matsala! Ita ce bayyanar kadoji ko ina, wadda ba mu taɓa gani ba a garin. Wannan ya sanya mu cikin firgici.

Ba damar zuwa saye-saye, yaranmu ba sa iya zuwa makaranta.

Alaramma ya yi ta jan hankulan jama'a cewa wanna jarrabawa ce daga Allah don ya gwada ƙarfin imaninmu, wani boka ne kawai da yaransa guda takwas, suka yi farin ciki. Abin alheri ya zama annoba. A hankali sai Allah Ya kawo sauƙi. Mutane sukayi murna. Boka kuwa ya kama baƙin ciki.

------------------------------------------------------------



Fati yarinya ce karama wanda ke gudu kamar
  iska.
  

  Tana son yin dariya kuma tana qoqari
  Kaman yadda aka umarce ta.

Yau ranar wassanin makaranta ne.
  

  Fati na wasan kwallon qafa
  kuma tayi wasannin gudu kashi uku.

Bayan makaranta, ta tafi gida tare da baban qawan
  ta Hawa.
  

  Hawa ta ce, “Fati, ki na gudu da sauri!”

Fati ta iso gida ta tarar da mamanta tana
  shirye-shiryen abinci.
  

  Ta ce, “Mama, ina ini.”
  

  Maman Fati ta amsa, “Ina ini. Yaya kike?”

Fati ta ce, “Yau mun yi wasannin makaranta. Na
  yi gudu sosoi.
  

  Ina jin zafi, na gaji kuma ina jin yunwa.”

Mama ta yi dariya, “Ta ce yar lele Fati na, an
  haifeki da saurin qafa!”
  

  “zan yi miyan kuvewa
  kuma abinci zai nuna bada daxewa ba.”

Mama ta sa dan man ja a cikin baban tukunya ta
  aza bisa wuta.
  

  Lokacin da manjan ta yi zafi, sai ta yanka
  albasa da tafarnuwa ta kuma juya kayan miyan har ya yi laushi.
  

  Sai ta sa barkono, tumatiri da dan ruwa. Sai
  kuma ta kara qwayan naman SA guda
  shida.

Mama ta ce, “Fati, ki kula ki dinga juya
  miyan.”
  Fati ta ce, “ Toh, mama.”

Fati ta juya miyan sau xaya.
  

  Sai tace, “Miyan na kamshin daxi.”

Fati ta juya miyan sau biyu.
  

  Sai tace, “Wannan miyan da xanxanon
  daxi.”

Fati ta juya miyan sau uku.
  

  Sai tace, “Wannan miyan gaskiya da daxi!”

Fati ta kalli maman ta.
  

  Mamanta ba ta kallon ta. Tana yankan alaiho da
  za ta sa a miya.

Fati ta dauki kwayan nama xaya
  daga tukunyan miyan ta ci.
  

  “Mmm,” ta ce.

Sai Fati kuma ta dubi mamanta.
  

  Mamanta ba ta kallon ta. Tana yanka kwai da za
  ta haxa cikin miyan.

Fati da wuri ta dauki nama na biyu daga cikin
  tukunyan miyan ta ci.
  

  “Mmm. Mmm,” ta ce.

Fati ta kuma duban mamanta.
  

  Mamanta ba ta kallonta. Tana yankan kuvewa
  da za ta haxa a miyan.

Fati da wurwuri ta xauki
  nama na uku daga cikin tukunyan miya ta ci.
  

  “Mmm. Mmm. Mmm!” Fati ta ce.

Mama ta zo bakin murhu da koren ganye, da kwai
  da kuvewa.
  

  Fati na nan rike da baban chokalin katako.

Mama ta yi murmushi, “Na gode da juya wannan
  miyan Fati.”
  

  Fati ba ta san abin da za ta ce ba.

Mama ta sa koren ganye, kwai da kuvewa
  a cikin miya.
  

  Ta karbi chokali daga hannun fati ta fara juya
  miyan.

Mama ta kalli cikin tukunyan miyan. Tana ganin
  miyan na tafasa a kan wuta.
  

  Mama tana neman kayan nama shida da ke cikin
  tukunyan miyan.
  “Xaya, biyu, uku.” Mama
  ta ga kwayan nama uku kawai a cikin tukunyan miyan.
  

  Mama ba ta ce komai ba. Fati ba ta ce komai
  ba.

Da mama ta raba abinci, Fati bata samu nama
  ba.
  

  Fati ta ce, “Mama, yi haquri.
  Ba zan qara yi ba.”
  

  Ba ta qara yi ba. Wannan shi
  ne qarshe.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci mai tsawo an yi wata mage mai wayo da wani dolon kare.

Ita magen tana rayuwa mai kyau a gidan masu kuɗi. Shi kuwa wannan dolon karen yana zaune cikin yunwa a kan hanya.

Dolon karen nan cikin fushi, sai ya tambayi wannan mage mai wayon ya ce, "Wai ta ya aka yi waɗannan masu arziƙin suka bar ki kike rayuwa a gidansu?"

Ita ko mage mai wayo sai ta ce da shi, "Ina rayuwa da mutane ne saboda tsaftata. Kuma ina binne kashina, kuma idan ina buƙatar abinci ina tambaya ne da cewa meow."

Karen nan ya ce, "Idan na yi kamar hakan shin za su bar ni in rayu a gidan?"

Sai mage ta ce, "E mana, ka yi kamar yadda na gaya maka za su bar ka kuma za su ba ka abinci."

Wannan dolon karen ya ce da mage, "Yau ba zan cutar da ke ba."

Sai magen nan ta ce yayin da take tsalle don barin wajen, "Cab yau kam ya kusa kama ni, amma ba zan sake yarda na haɗu da shi ba."

Saboda shawarar nan da mage ta bayar, sai dolon karen nan yaje g ƙofar wani gida ya dinga haushi da ƙarfi.

Sai masu gidan suka zane shi da sanda.

Sai wawan karen nan ya faɗa da ƙarfi ya ce, "Magen nan ta mai da ni wawa, sai na cinye ta idan na kama ta."

Yayin da magen nan take cikin wasa a wajen gidanta, sai karen nan ya yi carab ya damƙe ta.

Ya ce, "Wancan lokacin kin mai da ni wawa, kika ce min na yi haushi a ƙofar gida."

Masu gidan suka dake ni, yanzu sai na cinye ki.

Yayin da magen nan take cikin wasa a wajen gidanta, sai karen nan ya yi carab ya damƙe ta.

Ya ce, "Wancan lokacin kin mai da ni wawa, kika ce min na yi haushi a ƙofar gida."

Masu gidan suka dake ni, yanzu sai na cinye ki.

Sai karen ya tambaya, "Yaya ɓeran yake wasan?"

Sai magen ta amsa ta ce, "Ina ce masa ya yi tafiya, ya ƙirga uku, yayin da yake ƙirgen sai na kama shi."

Sai wannan dolon karen ya saki mage ta tafi, ya ce ta ƙirga uku.

Magen nan mai wayo ta kuɓuta ta haye kan bishiya. 

Sai karen nan ya ce da ita ki sauko daga bishiyar nan ki ƙirga uku.

Sai mage mai wayo ta ce da karen nan, "Ji nan ba za ka ƙara kama ni ba, ni ba wawiya ba ce."

Za ka iya ƙirgawa sau ɗari ko dubu ko ma malala. Amma dai ba za ka ƙara iya kama ni ba.

------------------------------------------------------------



Кwan! Кwan!

"Waye a nan?" na yi tambaya cikin magagi.

"Ni ne," in ji wata murya mai rikitarwa.

"Kamar ya ni ne?" na tambaya.

"Na gaya maka dai ni ne," muryar ta sake faɗa.

"Ni ban san wani 'ni ne' ba," na ba shi amsa. 

Na duba sai na ga sauro a maƙale a jikin gadona.

"Toh, sunana Sau," muryar ta amsa da ƙarfi fiye da da, har cikin kunnena.

"Wane Sau ɗin?" na tambaya lokacin da nake duba ƙarƙashin gidan saurona.

"Sau…ro." A ƙarshe ya faɗa. Kawai sai na ji cizo a kunnena.

"Ah! Na yi tsalle na fara dubawa. "Za ka yi da na sani." Na faɗa da ƙarfi.

Cikin fushi na tashi daga kan gado, na kunna fitila.

Tun daga nan na ƙulla yaƙi da sauro mai abin haushi!

------------------------------------------------------------



Giwa guda ɗaya ta nufi wajen shan ruwa.

Raƙuman dawa guda biyu, suna tafiya shan ruwa bakin tafki.

Bakane guda uku da tsuntsaye huɗu su ma suna tafiya shan ruwa.

Barewa biyar da wasu Gwankaye guda shida na tafiya tafki shan ruwa.

Jakunan daji guda bakwai na gudu zuwa tafki don shan ruwa.

Kwaɗi guda takwas da kifaye tara na yin ninƙaya a cikin tafki.

Wani zaki ya yi gurnani. Shi ma yana son shan ruwa. Waye ba ya tsoron zaki?

Wata giwa bata jin tsoron zaki domin tana shan ruwa tare da zakin.

------------------------------------------------------------



Akwai wani mutum da karensa guda ɗaya.

Ya na son karensa matuƙa sosai.

Karen yana da ƙwazo ana aikensa kasuwa ya sayo nama.

Yana zuwa rijiya ya ɗebo ruwa.

Yana tsare duk kayan gida.

Wata rana mutumin nan ya yi wa karensa gagarumar godiya kasancewarsa amintacce.

Kare ya yi murna kuma ya ci gaba da aiki tuƙuru.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci, an yi wani gida da suka rayu cikin farin ciki.

Yaran ba su taɓa faɗa da junansu ba.

Suna taimakon iyayensu a gida da kuma waje.

Amma ba a barin su su je kusa da wuta.

Suna yin duk ayyukansu ne da daddare.

Saboda jikinsu na kitse ne.

Amma ɗaya daga cikin yaran yana son fita cikin hasken rana.

Wata rana sai ya ƙagu sosai don ya fita. 

Sai ɗan'uwansa da 'yar'uwarsa suka gargaɗe shi.

Amman ina! Sun makara.

Sai ya narke a cikin zafin rana.

Yaran kitsen sai suka kama kuka, ganin ɗan'uwansu yana narkewa.

Yaran kitsen sai suka kama kuka, ganin ɗan'uwansu yana narkewa.

Sai suka ɗauki tsuntsun ɗan'uwansu suka ɗora shi a kan wani dogon tsauni.

Yayin da rana ta ɗaga, sai ya tashi sama yana rera waƙa a cikin hasken safiya.

------------------------------------------------------------



Fati yarinya ce karama mai gudu
  kamar iska.
  

  Tana son yin dariya, kuma
  tana kokari Kaman yadda aka faxa mata.

Wata rana, Fati
  da mahaifinta sun je gona
  bisa keke don yin ciyawa.

Jim qadan, Fati ta gaji.
  Sai tace, “Baba, ina zufa kuma
  na gaji. Zan iya zama
  a karkashin bishiyan mangworo?”
  

  Baba yace, “ee Fati, zaki
  iya zama. Amma, ki kula,
  kar ki hau kowace bishiya
  yau.”

Fati ta zauna karkashin
  bishiyan mangwaro.
  Fati ta xaga kai sama. Sai ta hango daya, biyu, uku
  nunannun mangwaro!

Fati ta waiga ta kalli
  babanta. Yana aiki bai lura da ita
  ba.
  

  Sannu sannu, Fati
  ta fara hawan bishiyan mangoro. Sai ta tuno “Bari in zauna nan. Wannan wurin yana da kyan hutu don shan mangwaro.”
  

  Sai ta zauna ta sha.

Bayan ta gama shan mangwaron, Fati ta sauko kasa.
  

  Sai ta hangi wata
  itaciyar.
  

  Wannan itaciyar tana
  dauke da wani ruwa mai gangarowa
  daga bawon itacen.

Ruwan zuma ne! Fati
  na son ruwan zuma! Amma ba
  ta son zuma.
  

  Fati ta kalli sama
  sai ta ga yar zuma.

Fati ta tsamanci wannan
  yar zuma ce. Ba za ta harbe ni ba
  in na hau bishiyan don neman ruwan zuma.

Fati ta kalli babanta.
  Amma bai lura da ita ba.
  

  Sai Fati ta hau
  saman bishiya ta xebo ruwan
  zuma daga cikin ramin.

Fati ta ga ya
  dace, “Zan zauna nan don wajen na da kyan
  hutu kuma in sha zuma da yawa
  mai zaqi.”
  

  Sai ta zauna ta sha.

Bayan ta gama shan ruwan zuma,
  Fati ta sauko daga kan bishiyan.
  

  Sai ta ga zuma.
  Ashe su na da yawa! BZZZ! BZZZ! BZZZ!
  

  Fati ta gudu daga
  wurin zuman.

Fati ta ruga wajen
  babanta tana numfashi da haki.
  

  Babanta yace, “Fati,
  ina kika shiga?”
  
  
  Fati ba ta so ta fadi
  inda ta je ba.

Sai tace, “Dubi
  baba, ina da mangoro.
  Kana son ka ci?”
  

  Baba yace, “a’a nagode. Dole mu hanzarta zuwa gida yanzu. An
  kusan fara ruwa.”

Baban ya dauki Fati a bayan keken shi a hanyan
  su ta komawa gida. Can sai aka fara ruwa.

Baba ya garzaya da keke.
  

  Sai keken ta kauce
  hanya.
  

  HATSARI!

Keken ya faxa kan kafar Fati.

Your translated text

A gida, mama da kaka
  sun tambaya abin da ya gudana a gona.
  

  “Fati ta hau bishiya,” Baba ya ce.
  

  “Tsananin gudu da Baba yayi yasa muka fadi
  da keke har ya fada kan
  kafa na,” inji Fati.

“Wayyo Fati,” Inji mama.
  

  “Baiwar Allah Fati,” inji kaka. “Ya kamata mu kula da kafan ki.”
  

  Haka ya faru. Karshen kenan.

------------------------------------------------------------



Wani daji ne a a kan hanya da kura a ciki

Sai kura ta rinƙa kururuwa  a dajin don kada yanfashi su shigo

Ana nan, wata rana yanfashin suka shigo dajin da daddare

Amma suka kama barci. Ashe kurar ta hange su

Sai kurar ta tsirgo daga bishiya, yanfashi kuma suka farka suka ranta ta kare

Ashe da maciji a kusa da su a dajin

Sai macijin ya sari ɗaya, ɗayan kuma ya gudu.

------------------------------------------------------------



Babbar mota ɗaya ce tak a ƙauyen su Tanko. Babba ce, kuma shuɗiya. Tana da ƙara sosai.

Gobe za mu je gari, inji mahaifiyar Tanko. "Za mu sayo kayan makarantarka."

Tanko ya yi murna sosai. Za su yi tafiya a babbar shuɗiyar mota. Bai yi barci ba wannan daren.

Yayin da mahaifiyarsa ta je tada shi, Tanko ya rigya ya shirya.

Tanko da mahaifiyarsa sun je inda motar ke tsayawa. Sun jira babbar shuɗiyar mota, amma motar ba ta zo ba.

Wasu mutane sun isa wurin tsayawar mota. Suna ƙorafi  saboda motar ta makara. "Ina motar?" Suka tambaya.

Tanko ya damu. "Ba mu da damar zuwa gari," ya yi tunani. Ba zai samu kayan makaranta ba.

Wasu mutane suka haƙura, suka koma gida. Tanko ya yi kuka, bai son ya koma gida. "Za mu jira kaɗan," in ji mahaifiyarsa.

Nan take sai suka ji ƙara. Suka ga ƙura na tashi a sama. Motar tana zuwa!

Amma motar ba shuɗiya ba ce, ba ta da girma. Ita ja ce, kuma ƙarama. Mutane ba sa son shiga wannan motar.

"A shiga! A shiga!" Direba ya daka tsawa. "Yau mun makara sosai," ya gaya masu.

Tanko da mahaifiyarsa suka fara shiga. Nan da nan kowa ya shiga cikin jar mota.

Tanko ya duba ta taga, sai ya ga mutane da yawa a tashar motar.

Mutane da yawa suna gudu don su samu motar. Amma sun makara. Jar motar ta cika. Ta tafi zuwa gari.

"Ina babbar shuɗiyar motar?" Mahaifiyar Tanko ta tambaya. "Ta lalace," inji direba. "Ana gyaranta. Za ta zo gobe."

Tanko bai damu da launin motar ba. Kuma bai damu da girmanta ba. Wannan motar za ta je gari.

------------------------------------------------------------



A lokacin da,  an yi wata yarinya mai sunan Hadiza,  ta na rayuwa ne tare da uwayenta da suke kusa da garin budongo. Wata rana,  uwar Hadiza ta aike ta rijiya ɗibar ruwa.

Bisan hanyarta,  ta gamu da abokananta. Za su tafiya cikin daji neman itace. Hadiza tana son ta bi su. "Don Allah ku jirayeni ƙarƙashin iccen kuka!" in ji ta. "Za ni tafiya in ɗebo ma uwata ruwa." Amma abokananta ba su son su jiraye ta.

"Da kyau,  za ni cimmaku cikin daji" in ji Hadiza. Ta je da gudu ta ɗebo ruwan,  ta kawo ma uwarta. Kuma ta je cikin dajin ta tararda abokananta.

Ta bi ta hanyar da za ta kai ta wajen wani marmaro. Daga wata gaɓar ruwan,  akwai ƙananan hanyoyi da suke kai ka ko'ina. "Ta ina suka bi?" tana tambayar kanta.

Ta ɗauki hanyar da ta fi nisa,  take tafiya,  take tafiya,  amman ba ta cimma bokananta ba. Ta gaji ƙwarai sai ta zamna ƙarƙashin wata bushiya don ta futa,  daga nan kwana ya ɗauke ta.

Lokacin da Hadiza ta farka,  dare ya yi. Cikin dufu,  sai ta hango wasu idanu masarori suna walƙiya. Kuraye sun kewaye ta! Ta firgita sosai har ba ta iya kuwa. Ta so ta tsere amma kurayen da suka kewayeta suma yunwa suke ji.

"Kar da kimotsa" inji babban kuren,  da wata ƙwararar murya. "Idan kin yi gudu,  za mu cinye ki." Sai ta roƙe su,  "don Allah,  ku bar ni in tafi gidanmu!"

Amma maimakon haka, sai kurayen suka kai ta gidansu can cikin daji. Wani ɗaki ne mai dauɗa,  cike da ƙasusuwa sai ƙuda suna ta yin bobowa. Ta yi kwance kamar ta yi barci.

Cikin dufu,  ta ji kurayen suna yin shawara. "Yaya wutar?" wata kura ta tambaya. "Ko ruwan sun tafasa?" "Komi ya kammalu" aka bata amsa. "In janyo ta?" "e,  e!" sauran kurayen suna gurnani. "Yunwa muke ji!" Sun shirya su fito da Hadiza daga cikin ɗakin.

Sai babban kuren ya ce,  "Kai kuraye,  ku dakata. Kar kumanta ƙa'idar wannan garin. Babu kuren da za ya ci shi kaɗai. Ya kamata mu gayyaci duk iyalenmu don mu ci abincin." "Za ni gayyaci sirikaina" in ji matarshi. "Za ni je in kiranyo ƴan uwana" in ji ƙaramar kurar. "Ni ko za ni tsayawa don in fake abincinmu" in ji babban kuren.

Babban kure ya zauna bakin ƙofar ɗakin,  sauran ko suka barbazu cikin daji. Can da jimawa,  babban kure ya fara angaje gaban wutar da suka kunna. Nan take har ya fara shinkori. Sa'ar Hadiza ke nan! Amma,  yaya za ta bi kusan da kuren? Saboda girmanshi ya tare ƙofar fita.

Hanya guda ce,  ta tsalaka sama,  ta faɗa wancen ɓangaren na kuren,  sai ta zuba da gudu bakin ƙoƙarinta.

Ko da sauran kurayen suka dawo,  suka lura da abun da ya faru,  suka je neman Hadiza,  cikin baƙin-ciki da takaici. Amma,  ina,  ta yi nisa.

Da ta iso cikin garinsu,  wani mutum ya gane ta sai ya sa kuwa,  "Hadiza,  Hadiza ta dawo,  Hadiza ta dawo" Babanta da uwarta suka tarbe ta da gudu,  suka rungume ta,  su na yi wa Allah godiya da ya ceci diyarsu,  "Hadiza,  Hadiza,  mun aza kin mutu!"

Tun daga wanna ranar,  Hadiza da sauran yaran,  basu sake komawa cikin daji su kaɗai.

------------------------------------------------------------



Za su je wasa tare da giwa

Sun tafi wasa.

------------------------------------------------------------



Wannan ita ce Delu. Tana da 'yan uwa  guda shida.

Iyayenta sun ba ta ƙaramar tukunya. Tana son tukunyar.

Wata rana 'yan'uwanta suka fasa tukunyar.

Da Delu ta rasa tukunyarta, sai ta fashe da kuka.

Delu ta ruga da gudu. Ta hau kan doguwar bishiya.

Iyayenta suka nemi da ta yi haƙuri. Ta sauko daga kan bishiyar.

'Yan'uwanta suka yi mata waƙa. "Yi haƙuri ki sauko ƙasa."

Delu ta mayar da waƙarsu abin dariya.

Sannan, ƙawar Delu ta zo. ''Yi haƙuri ki sauko ƙasa.'' Ta rera waƙa.

Ƙawar Delu ta ci gaba da waƙa, har sai da ta sauko daga kan bishiya.

Suka tafi gida tare da ƙawayenta.

Kowa yana farin cikin dawowar Delu gida. Delu ta samu sabuwar tukunya.

------------------------------------------------------------



Bera yana neman sabon gidan da zai kwana.

Sai ya ga wani gida da ya birge shi.

"Za ka iya zuwa ka kwana a gidana," in ji Dankwikwiyo.
  
"Na gode," Bera ya ce.

A wannan daren bera bai yi barci ba sabo da hayaniyar kare.

Kashe-gari sai suka hadu da Aku, ya ce, "Za ka iya zuwa mu kwana tare."

Bera ya ce, "Na gode."

A wannan daren Bera bai yi barci ba sabo da surutun Aku.

Kashe-gari sai suka hadu da Kifi, ya ce, "Ya ce za ka iya zuwa mu kwana tare."

Bera ya ce, "Na gode."

A wanna daren Bera bai yi barci ba sabo sanyin ruwa.

Bera yana son gida mai dumi ne.

Bera yana neman sabon gidan da zai kwana.

Sai Bera ya samo wajen ajiye litattafai.

A wannan daren Bera ya yi barci mai dadi.

A sha barci lafiya Bera.

------------------------------------------------------------



Ga saniya. 

Saniya ba ta da damuwa.

Cikin wuni, saniya ce kamar kowace saniya.

Tana wasan jirgin kara.

Tana harba wani ƙwallo da ƙafa.

Amma da dare saniya ce mai ban shawa.

Tana ceton rayukka.

Tana yaƙar ta'addanci.

Idan ka rufe idanunka, kuma ka nemi wata buƙata.

Saniyar tana iya kuma kai ma ziyara!

Ƙarshe.

------------------------------------------------------------



Delu ta na kallon yara maza suna wasan ƙwallon ƙafa. Ta so a ce ta na cikin su. Ta tambayi maihorar da 'yanwasan, "Ko za ta iya shiga cikinsu ta yi wasa?"

Maihorar da 'yanwasa ya riƙe hannuwansa akan ƙugunsa ya ce, "A wannan makaranta maza ne kaɗai ake bari su yi wasan ƙwallon ƙafa."

'Yanmaza suka ce mata ta ta tafi ta yi wasan ƙwallon raga, ita ce ta mata, ƙwallon ƙafa ta maza ce. Delu ta damu.

Washe gari, makarantar za ta yi babban wasa. Maihorar da 'yanwasa ya damu saboda ƙwararren Danwasan sa ba ya da lafiya kuma ba zai iya wasa ba.

Delu ta ruga wajen maihorar da 'yanwasa ta roƙe shi ya kyale ta, ta yi wasa. Maihorar da 'yanwasa ya rasa yadda zai yi. Sai ya yanke shawra Delu ta shiga cikin su.

Wasa ta yi zafi, ba wanda ya ci ƙwallo a farkon rabin lokaci.

Lokacin da aka juya rabin lokaci na biyu, sai wani daga cikin su ya turawa Delu ƙwallo. Sai ta ruga da sauri kusa da ƙwallo. Delu ta doki ƙwallo da ƙarfi ta ci.

'Yankallo suka miƙe da murna. Tun daga ranar aka ƙyale mata suna yin wasan ƙwallan ƙafa a wannan makaranta.

------------------------------------------------------------



Ƙauna an haife ta ba ta gani. Ba ta taba ganin Iyayenta ba, ko kuma 'yan uwanta. Amma ta san fuskokinsu domin tana taɓawa.

Wata rana, Ƙauna ta je lambu. Ta na son ta shaƙi ƙanshin fure. Tana kuma son taɓa su.

Ƙauna tana sha'awar ta ga furanni ko da sau ɗaya ne. Ta faɗa a cikin ranta, "Furanni suna da kyau."

Kullum, Ƙauna takan je lambu. Ta gane duka hanyoyin lambun. Yau, ta ɗaga kanta ta kalli sama.

Ba shiri kawai sai ga tsawa da walƙiya. 

"Bari in yi hanzari in koma gida," Ƙauna ta yi tunani.

Ruwan Sama ƴa fara zuba. Ƙauna ta faɗi a ƙasa, kanta ƴa bugu da dutse.

Da Ƙauna ta buɗe idanunta, ta kalli mutane sun kewaƴe ta. "Me ƴa faru?" ta tambaƴa.

Babanta ƴa ce. "Ƙin faɗi kin ɓuge kanki ne."

"Mun gode Allah kina lafiƴa," mamanta ta faɗa.

"Baba, Mama?" Ƙauna ta kuma kiran sunan 'yan uwanta. "Don Allah a samo mini fure."

Mamaki ƴa kama sauran 'yan uwanta.

Da 'ƴar uwan ta ta dawo da fure, Ƙauna ta riƙeshi a hankali. "Fure na da ban sha'awa," ta ce.

Ýan uwanta suka kalli juna. 

"Ƙauna, ƴanzu kina iya ganin furen?"

Ƙauna ta yi murmushi, ta ce, "Dukan ku kuna da kyawun gani, kamar furen nan."

------------------------------------------------------------



Damina ba ta sauka ba, saboda haka ƙasa ta bushe.

Wannan biranyar ta bar gida don neman ruwa da abinci.

Tana kai-kawo cikin tudu da kwari.

Sai ta iso  wani wuri da ake kira Tirkol.

Biranyar ta yi farin cikin isa  wannan wurin.

Ta ci 'ya'yan itace ta yi ɓulɓul. Sai dai, ta yi kewar ƙawayenta.

Don haka, biranyar ta kama hanyar gida.

Sauran biran suka cika da farin cikin ganinta.

Suka tambaye ta, "A ina wannan ƙasaitaccen wuri mai 'ya'yan itatuwa yake?"

"Zan kai ku wajen," cewar biranyar.

Sauran biran suna ƙaunar Tirkol. Sai suka ƙuduri zamansu a nan har abada.

Amma biran Tirkol sai suka damu.

Suka ce, "Waɗannan baƙin biran za su cinye mana duk abincinmu."

Don haka,  biran Tirkol sai suka kai wa  baƙin birannan farmaki.

"Me zai sa mu yi  fada?" Wani a cikinsu ya ce, bayan akwai abinci mai yawa.

Wannan haka ne. Sai suka ƙudurta su zauna tare cikin lumana.

------------------------------------------------------------



Anansi Gizo ne raggo.

Yana son abinci, amma raggwancinsa kan hana shi girki.

Anansi ya ziyarci zomo, ya ce, "In zo muci kayan lambu?"

Zomo ya ce, "Eh! sai dai ka taya ni juya miyar." Amma Anansi raggo ne.

Anansi  ya ce, "Bari in dawo."

Anansi ya saka yana a ƙafarsa da jikin tukunyar zomo.

"Ka ja yanar idan kayan lambun sun nuna," inji Anansi.

Ya ƙara gaba, "Birai, in zo mu ci wakenku?" "Eh! Ka taya mu dafawa "

"Zan dawo," inji Anansi. Ya kuma sake saka yana.

"Gwanki, in zo muci dankalinka?" "Eh! Taimaka mini mu shirya abinci."

"Zan dawo," inji Anansi. Ya kuma sake saka yana.

Jim kaɗan, kowace ƙafa daga ƙafafuwan Anansi 8 an ɗaure ta a jikin tukunya.

Anansi yaji anja ƙafarsa ta 2, Sannan ta 3.

Duka ƙafafuwan 8 a ka dinga jan su! "Ku bar ja!" Anansi ya fasa kuka.

Ba wanda yaji kukan Anansi.

Ƙafafun Anansi suka miƙe! Wannan ya sa ƙafar Gizo ta zama siririya.

------------------------------------------------------------



Kai! Akwai saniya mai kyau a gidan mu.

Ta na da ƙaho daya kuma ba ta da jela.

Ta na da ƙiba da ƙaton ciki.

Saniyar tana da ƙarfi sosai.

Makiyayinmu na son wannan saniya matuƙa.

Yayin da sauran shanu ke yin kiwo tare, ita ta kan yi kiwo a ware.

Wannan Saniya mafaɗaciya ce, don haka sauran shanu suke ƙaurace mata.

Idan ka haɗu da irin wannan saniyar, yaya za ka yi?

------------------------------------------------------------



Kaza da shanshani abokai ne. Amma kullum suna takara tsakaninsu. Wata rana, sai suka yi niyyar wasan ƙwallon ƙafa don sanin wa ya fi kwaninta tsakani su biyu (2).

Sai suka shiga filin ƙwallon ƙafar kuma suka fara wasan. Kaza tana da gaugawa amma shanshani ta fi ta gaugawar. Kaza ta harba ƙwallon nesa amma kuma shanshani tana aika ƙwallon neza ƙwarai fiye inda na kazar zai je. Ganin haka, sai kaza ta fara hassala.

Ƴan takarar biyu (2) sun yi niyyar su je bugun da kai sai mai tsoron gida. Da farko shanshani ita ce mai tsaron gida wato gola kenan. Kaza ta saka ƙwallo ɗaya rak cikin raga. Sai aka juya, kaza ta zama gola mai tsaron gida.

Shanshani ta harba ƙwallo, kuma ta saka a raga. Shanshani tana gwaninta kuma tana saka ƙwallon. Shanshani ta saka ƙwallon har da kai. Shanshani ta saka ƙwallon biyar (5).

Kaza ta hassala da rishin nasarar da ta yi. Kaza ba ta iya wasa ba. Shanshani ta yi ta dariya saboba abokiyarta ta hassala wajen wasa.

Sai kaza ta buɗe babban bakinta ta haɗiye shanshanin.

Lokacin da kaza tana shigowa gida, sai ta gamu da uwar shanshani. Sai ta ce mata, "Ba ki ga ɗiyata ba?" Kaza ba ta amsa mata ba. Uwar shanshani ta damu.

Sai uwar shanshani take ji wata ƙaramar murya tana cewa: "Ki agaje ni uwata!" Shanshani take faɗi. Uwar shanshani ta duba kewayenta da kyau. Muryar nan da cikin kaza ta fito.

Uwar shanshanin ta yi ihu, "Ki yi amfani da duk azirinki ɗiyata!" Shanshani ta saki wani wari. Sai kaza ta fara jin wani ciwon ciki.

Kaza ta yi gyatsa. Kuma ta yi kaki. Ta yi attishewa kuma take ta tari, take tari. Shanshani bai ciyuwa!

Kaza ta yi ta tari sai ta kako shanshanin da yake cikin cikinta. Shanshanin da uwarta sun tafi sun ɓoye cikin wani icce.

Tun daga shi, kaza da shanshani ba su shiri.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci mai tsawo da ya wuce, an yi wasu matasa guda biyu waɗanda suka rasa shanunsu.

Sun yi ta neman shanun har zuwa yamma.

Da duhu ya kawo kai sai suka hango wani haske a wani gida. 

Sai suka shawarta cewa su je su tambayi wajen kwana.

Suka ƙarasa zuwa gidan suka ƙwanƙwasa ƙofar. Sai kuwa ƙofar ta buɗe suka kutsa kai ciki.

Matasan nan ba su ga kowa ba, sai wata murya suka ji tana gaishe su.

Sai muryar ta ce da su, "Ni kwarkwata ce, ku buɗe tukunyar ƙarfen nan akwai abinci ku ci, sannan ga ruwa nan a cikin randa ku sha."

Sai kwarkwatar nan ta saka fatarta ta fice.

Matasan nan suka ci suka sha kuma suka yi godiya. 

Sannan suka suka bar gidan.

Daga tafiyarsu, sai wani mummunan tunani ya zo musu cewa, "Ba zai yiwu ba a ce wai kwarkwata ce ta ba mu abinci."

Kawai sai suka shawarta cewa su koma su muttsuke wannan kwarkwatar.

Suka dawo gidan suka muttsuke kwarkwatar.

Kawai sai suka tarar babu kwarkwatar, kuma gidan ma ya ɓace.

Sai kuwa suka samu kansu a wani fili fetal.

------------------------------------------------------------



Ga Giwa! Ga Giwa!

Wannan Giwar ita kadai ce a cikin dajin nan.

Wannan dajin sunan shi Kibale.

Giwar ta je shan ruwa a rafi.

Yara na wanka a rafin.

Yara sun ruga suna cewa, "Ga giwa! Ga giwa."

------------------------------------------------------------



A wani lokaci daya yawuce. Anyi wani yaro mai suna Babangida. Babangida ya kasance ba shida kyawun hali domin kullum ba shi da aiki sai yi wa yara 'yan uwansa mugunta ga shi Da stokana da kuma keta.

Idan wani abin bacin rai ya samu wani Daga cikin yara, Sai Babangida ya yi ta mass dariya Yana stokana.

Malamar su Babangida ta sha yi masa faɗa. Amma Babangida ba ya Jin maganarta, domin ya raina duk nagaba da shi.

Wata rana Babangida Yana cikin aji tare dasauran yara Suna daukar darasi Sai fistari ya kama Babangida.

Babangida ya nemi izini malamarsu domin ya je ya yi fistari, Amma Sai malamar ta hana Shi fita. Domin ta dauka Babangida Yana yin shakiyanci ne Kamar yadda ya saba.

Sai Babangida ya sake neman izini a wajen malamarsu. Amma malama ba ta ba shi izini ba. Ga shi Kuma fistari ya maste Shi.

Can Sai Babangida yakasa jurewa har yayi fistari a wando ya bata wandonsa kuma ya bata wajen zamansa.

Ko da sauran Yara suka ga abin da ya Samu Babangida sai suka fashe da dariya, suka yi ta nunashi suna stokanar sa. Har ma suka fara yiwa Babangida Waka, Suna cewa "Amalala Mai fistarin zaune" Sai Babangida ya fashe da kuka.

Koh da malamar su Babangida ta ga abin da yake faruwa, sai ta stawatar wa Da sauran Yara, ta Kuma yi musu gargaɗi a kan stokanar Babangida

Sai malama ta bai wa Babangida izini domin ya je ya wanke jikinsa, Babangida ya ji kunya sosai a ranar. Kuma ya ji ba dadi a lokacin da yara suke stokanar sa.

Sai Babangida ya faɗa a ransa cewa "Au a she haka yara suke ji idan na ci zarafinsu koh na stokanesu?"

Tin daga ranar Sai Babangida ya chanja halayensa ya kuma yi alkawarin ba zai sake yin stokana da cin zarafin wani ba.

------------------------------------------------------------



Da hancina.

Ina jin warin suseti masu dauɗa.

Ina jin ƙamshin hure mai kyau.

Da idanuna.

Ina ganin wani ƙwallo ta tashi sama,  sama ƙwarai cikin iska.

Ina ganin wata mussa cikin farin rai.

Da bakina.

Ina ɗanɗana ruwan teku masu ɗanɗanon gishiri.

Ina ɗanɗana ruwan lemu mai sukari.

Da hannuna.

Ina riƙe hannunka.

------------------------------------------------------------



Wata yarinya iyayenta suka aike ta wajen kakanta da ya ke zaune a cikin daji. Ta tafi cikin farin cikinta.

Lokacin da ta isa kusa da daji, ta haɗu  da wata akuya ta yi mata magana cewa ta yi a hankali domin za ta haɗu da namun daji.

Lokacin da ta kai tsakiyar dajin, ta samu namun daji da yawa a kusa da hanya, sai ta yi ta gudu tana ƙara.

Bayan ta fita daga daji, sai ta haɗu da tsuntsaye masu yawa a waje guda suna ƙara, sai ta ƙara gudu tana ƙara. Sai kakanta ya jiyo ta.

Kakanta ya ce da matarsa wannan jikarsu ce. Ya fita da sauri tare da karensa domin duba ta kuma ya same ta a gajiye.

Lokacinda suka isa ta shiga gida ta gaishe da sauran yara kuma ta ɗauki abinci. Bayan ta gama cin abinci ta ba su labarin abin da ya faru a kan hanya.

Bayan fadɗn abinda ya faru sai aka ba ta shawara ka da ta ƙara biyowa ta cikin daji ba tare da wani ba, sai ta tafi cikin farin ciki sukai ta wasa da sauran yara.

Ba ta sake biyowa ta cikin dajin ba tare mai rakkiya ba.

------------------------------------------------------------



Wata rana bayan ɗaukewar ruwan sama, Iman ta kalli sama ta ga launuka a karon farko.

Ta yi tunanin cewa babu wani abu mai kyau kamar wannan. Dole ne a samu, wanda ya yi fentin sararin sama kamar yadda Baba ke fentin gidaje.

Ta gudu zuwa wurin 'ƴar'uwan ta, ta ce, "Zarah, kalli! Wani ya mana fentin sararin sama kuma ya yi kyau sosai."

Sai Zarah ta ce, "A'a. Wannan bakan-gizo ne. Ke ƙarama ce, kuma ni babba ce. Na san dalilin da ya sa yake sama. Bari in nuna miki."

Zarah ta ɗauki Iman zuwa gidan namun daji. Ta ce, "Bakan-gizo basa fitowa saboda kukan zaki, ko saboda haihuwan giwa."

Ta ɗauki Iman zuwa filin furanni. Ta ce, "Ba su fitowa saboda malam buɗe littafi, su kan tashi sama kuma launukansu su kan watsuwa a sama."

Ta nuna ma ta littafi. Ta ce, "Basu fitowa saboda kakandai sun gudu a ƙasa kuma sun tsorata launuka har zuwa sama."

"Na san dalilin da ya sa bakan-gizo kan fito sararin samaniya. Mama ta gaya min, kuma zan gaya miki." Zarah ta kai Iman zuwa filin wasa.

"Bakan-gizo sukan fito saboda yara kamar ni da ke. Wata rana, launuka suka kalli ƙasa, kuma su ka ji suna son abin da suka gani."

"Suna ganin yara da hasken fata, da masu baƙin fata, da duk abin da yake tsakanin su. Su ka yi tunani, zai zama abun farin ciki mu yi kyau kamar su."

"Sa'annan suka yi shawaai akan abin da za su yi. 'Idan za mu yi kyau kamar su, sai mun haɗa launukan mu.'"

"Daga wannan lokacin, ya zamo suna haɗa launukan su, su yi haske kamar yara."

------------------------------------------------------------



Kalli dabbobin da mu ke kiwo a gida.

Saniya tana bamu madara.

Zomayye da mage abokan mutane ne.

Doki yana haniniya ya ce, "Ehhehhh."

A ƙasar Uganda ana bayar da shanu da awaki a matsayin sadaki.

Kaza tana cewa, "Kuut-ƙuut."

Ana amfani da kare a matsayin mai tsaro a gidajen mu.

Manomi yana kula da dukkan dabbobi sosai.

------------------------------------------------------------



Litinin da ta wuce,  Nakitto ta fara zuwa makaranta.

Ta zo cikin sabon aji kuma ta yi sabbin abokai.

Rabiya tana son littattafai masu hotuna.

Ƴan makaranta sun fito waje don su goyi wasu darussa.

Sun goyi sautin haruffa.

Sun futa bayan sun yi karatu. 

Rabiya ta yi barci kusa da malama.

Suna kuma yawon ƙara sani.

Rabiya tana karatu tare da ma'aifiyarta a gida.

------------------------------------------------------------



Akwai wata yarinya, sunan ta Ayanda.

 Ayanda ita ce kaxai yarinya iyaye'n ta.
  
Mama'n ta xa Baba'n ta sun so su rabu.

Ayanda ta yanke shawara za ta gudu xaga gida.
  
Ta shige kurmi domin ba ta san wuri'n xa za ta je ba.

Kyarkeci a kurmi ya kore Ayanda, sai ta hau bishiya.
  
Kyarkeci ya yi kokarin cizo'n ta, sai ta ka ra hawa sama.

A sama'n bishiaya'n, Sai Ayanda ta gan kyakyawan rana.
  
Ta fara sha'awan ranan, sai ta yanke shawara'n zama a' kurmin.

Ayanda ta hau bishiyan kowane rana ta yi Magana xa rana'n.
  
Sai Rana ya zama iyali'n ta.

Wata rana, Ayanda ta gan wani mutum a karkashin bishiyan.
  
Mutumi'n Baba'nta ne Ayanda ta soko kasa daga bishiya sai bava'n ta ya bayyana dalilin ya sa ya na wurin.

Ya faxi, "tun kafin a haife ki, mama'r ki xa ni zamu gamu a nan. Nan wuri, na musamman ne."
  
"yanzu na hau bishiya na samu qwanciya'n hankali
  a lokacin da mama'r ki xa ni mu yi faxa", in ji Baba'n Ayanda.

Bayyan wani lokaci, Mama'n Ayanda ita ma ta zo kurmi'n.
  
Ta zo ta yi zaman lafiya da baba'n Ayanda.
  
Wannan shi ne bishiyan lafiyan su.

------------------------------------------------------------



An yi wata ƙaramar yarinya da ake kira Fati. Bayan rasuwar ma'aifin, Fati ta zamna tare da ma'aifiyarta. Wata rana, ma'aifiyarta ta ce mata, za ta ƙaura ta koma wani gari don ta sake wata sabuwar rayuwa.

Fati ko ba ta son barin garinsu, kuma sai ta yi ta kuka. Ma'aifiyarta ta ji tsoron barin ta ita kaɗai,  saboda garin akwai ƙatti da suke ci. Amma Fati ta yi ta kuka har sai da ma'aifiyar ta yarda ta bar ta.

Ma'aifiyar ta ɗauki alkwalin kai ma ɗiyarta abinci kullum. "Zan yi waƙar da za ki gane ni in na zo. Amma kar ki buɗe ma kowa ƙofa," in ji uwar Fati.

Fati ɗiyata! Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki! Fati ɗiyata! Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki!

Washe gari, ma'aifiyar Fati ta zo ta kawo ma ɗiyarta abinci. Ta fara waƙa: Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fati ta buɗe ƙofa ta ci abincinta mai daɗi.

Ma'aifiyarta ta sumbace ta, kuma ta koma garinta. Fati ta koma ɗakinta ya kwanta. Ashe wani ƙato yana laɓe bayan wani icce, yana saurare Fati da ma'aifiyarta!

Lokacin da Fati ta kashe fitila sai ta ji wata babbar murya, na rera waƙar da ma'aifiyarta take bakin ƙofarta. Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! "Tafi ka ba ni wuri! Wannan ba ma'aifiyata ba ce," in ji Fati. "Kai ƙato ne!" ƙato ya tafiyar shi cikin ɓacin rai. Ya koma cikin gidanshi na dutsi.

Kullum safe da maraice, ma'aifiyar Fati tana kawo mata abinci. Kullum safe da maraice, ƙato ya na zuwa shi ma. Amma kullum Fati na korar shi. Tana gane shi ta babbar muryarshi lokacin da yake kokoyon waƙar.

Wata rana, ƙato ya yi tunani ya ce: "Ina iya sauya muryata don ta zama kamar ta ma'aifiyar Fati." Sai ya fura wuta da yawa kuma saka dutsi mai sulɓi cikin wutar. Bayan dutsin ya yi zafi, sai ya fiddo shi ya hadiye shi! "Gulugulu!" Dutsin ya wuce ta maƙogoron ƙaton.

Ƙato ya fara waƙa don ya ji in muryarshi ta sake. 
Ya yi ta jin daɗi ya ji muryar tashi ta yi kama da ta ma'aifiayar Fati!

Washe gari, ƙato ya je bakin ƙofar Fati. Ya fara waƙar kamar haka: Fati ɗiyata! Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki!

Fati ta ji daɗi da ji muryar ma'aifiyarta. Da buɗe ƙofa,  sai ga ƙato! Sai ta so ta rufe ƙofar amma ƙato ya fi ƙarfinta! Ya ɗauki Fati ya saka ta cikin buhu.

Ƙato ya nufi hanyar gidan shi na dutsi, kuma yana waƙar jin daɗi. "In dama ina da giyar burkutu, da na ji daɗin abincina da dare! Yau sai na ji daɗi!" yake faɗi.

Can da hantsi, ma'aifiyar Fati ta zo ta kawo mata abincin kamar yadda ta saba kullum. Ta rera waƙar,  amma Fati ba ta fito ba. Ta sake rera waƙar, Fati ba ta amsa ba, shiru! Bayan na ukku, sai ta tura ƙofar. Babu Fati. Sai ta yi mamakin abin da yake iya faruwa, sai ta yi tunani da gaugawa don samun wata dubara.

Sai ta cika wata ƙwarya da giyar burkutu ta ɗaura saman kai,  ta tafi wajen gidan ƙato kuma ta sallama mishi. Ƙato da ya ji ƙamshi burkuntun sai buɗe ƙofar ba da ɓata lokaci ba. "Ina wuni ƙato!" in ji ma'aifiyar Fati. "Ina wucewa na ji kana waƙa da kyau. Yanzu zan je wani garin wajen bikin zagayowar shekarar aifuwar wata ɗiyata."

Ƙato ba zay barin wannan damar da aka ba shi ta ya sha giyar burkutun! Sai ya sabkar da ma'aifiyar Fati gidanshi. "Bari in zuba maka giyar kafin in wuce." In ji ma'aifiyar Fati. Ƙato yana jin daɗi ya samu giya.

Ma'aifiyar Fati tana zuba mishi yana sha, yana ta sha sai da ya shanye duk ƙwaryar. Yanzu ƙato ya yi tilip! Yana yin maye har barci ya kwashe shi.

Lokacin da ma'aifiyar Fati ta ji ƙato ya fara shinkori,  sai ta buɗe buhun suka gudu da ita da Fati. Fati da ma'aifiyarta sun gudu sun koma gida. Tun daga ranar nan, Fati take tare da ma'aifiyarta cikin sabon garinsu!

------------------------------------------------------------



Afeefah wata ƙaramar farar karkanda ce.

Masu taimako sun kawo mata agaji daga daji.

Mafarauta sun kashe mata mahaifiyarta.

 Masu taimako sun kai Afeefah wani waje mai tsaro.

Zuciyar Afeefah ta karaya.

Sannan kuma tana tsoron kar mafarautan su dawo su ɗauke mata ƙahonta.

A hankali, Afeefah ta samu ƙawaye.

Ta ji ta samu tsaro, har ta yi wasa a cikin taɓo.

 Kuma ta sha madara mai gina jiki a waje mai tsaro.

Wata rana sai Afeefah ta tambayi ƙawarta Aminaah. "Wai me ya sa suke son ƙahonmu ne?"

Aminaah ta yi wani huci ta ce, "Sun yarda wai ƙahonmu ana tsafi da shi."

Afeefah ta yi kuka ta ce, "To ai ƙahonmu ba na tsafi ba ne."

Sai Ameenah ta ce, "A'a tabbas ba haka ba ne, ƙahonmu daidai yake da gashi da farce."

Afeefah da Ameenah su ne na ƙarshen a irinsu. 

Duk fararen karkanda sun kusan ƙarewa.

Kusan duka ma sun bar duniya.

Za mu iya ceto karakandai da kuma sauran dabbobin da suka kusa ƙarewa. 

Me za ku iya iyi? 

Ku nemo sauran.

------------------------------------------------------------



A wani gari mai suna Magarya. An yi wani mutum mai suna Bunu.

A garin Magarya, masana labarai suke bada labarai masu qayatarwa.

Da aka zo kan Bunu, sai ya ce, "Labarina a kan Damisa ne."

Yana fadin kan labarinsa, sai kowa ya yi shuru ya kuma saurara.

Bunu ya gyara murya ya ce, "Damisa kamar Kyanwa ta ke."

Sai kowa ya ce, "Lallai, haka ne."

Kuma ya ce, "Damisa na da tsawon bindi."

Sai masu saurare suka ce, "Ummm, gaskiya ne!"

Lokacin da Bunu ya fahimci ya fara birge jama'a.

Sai ya yi farat kamar qorarren mai bada labari, ya ce, "Ai lokacin da muke yara, malamin mu ya kai mu bakin rafi ya nuna mana Damisa."

Ita Damisa tana da qaho biyu irin na Barewa.

Sai kowa ya kyalkyace da dariya yana yi masa ba'a.

"Bunu makaryaci ne, kuma bai san yanda Damisa take ba."

Bunu ya gane kuskuren sa sai ya ce, "Daga yau ba zan
sake ba da labarin abinda ban sani ba."

------------------------------------------------------------



Fati karamar yarinya
  ce mai gudu kamar iska.
  

  Ta kan so dariya, kuma ta kan yi haka
  Kamar yadda aka so.

Wata rana Fati
  da maman ta da baban ta, su ka je neman
  itace.

Fati ta kan so taimakon
  mamman ta da babban ta, amma akwai abubuwa
  da yawa na gani da koyo.
  

  Akwai tsuntsaye, burai
  da sararin sama.

Mama ta ce, “Fati saurara! Za ki iya
  neman itace anan da can.”

Amma Fati, Kalli
  inda za ki kuma ki
  yi hankali.”
  

  Sai ta ce, “Na ji
  mama.”

Can sai maman Fati da Baban suna cikin
  aiki.

Sun samu babban itatuwa.
  

  Saun samu kananan
  itatuwa.

Fati ma tana cikin
  aiki.
  

  Ita ma ta samo yan
  itatuwa.
  

  Ta samu kananun itatuwa sosai.

Sai Fati ta kalli
  sama.
  

  Sai ta ga jan tsuntu akan doguwar
  ciyawa.

Sai Fati ta kalli
  kasa.
  

  Sai ta ga tururuwa
  a cikin rairayi.

Fati ta ga ganye
  mai kyau. Ganyen na shaiki
  kuma kore shar.
  

  Sai ta sa yatsa
  daya akan ganyen,

Fati tace, “Wannan
  ba yi kama
  da ganye ba.”
  

  Nan take, sai ta ga ganyen mai
  kyau yayi motsi.
  

  Fati tace, “Wannan
  ba ganye ne mai kyau ba.
  Wannan koren maciji ne!”

Fati ta yi ihu,
  “Wayoo!”
  

  Sai ta ruga da gudu
  zuwa neman babbanta da mammanta.

Fati ta ga babbanta
  sai ta yi ihu, “Maciji! Maciji!”
  

  Babbanta yace, “Ina yake?
  Ina yake?”
  

  Fati ta ce, “Ga shi can! Ga shi
  can!”

Sai babanta ya kori koren macijin
  da sanda.
  

  Koren macijin ya subule.

Baba yace, “Fati, Allah ya tsare ki.
  

  Muje gurin mama, mu sanar
  da ita game da koren maciji.

Mama ta ce, “Fati, ina miki
  murna da koren macijin bai cije
  ki ba.”

Amma nan gaba, ki
  kula da inda kike zuwa, kuma ki
  yi hankali.”
  

  Kuma karshen kenan.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci can daya shude, dabbobi sukan yi magana. Zomo da kura sun zauna a wani wuri.

Sun yi abuta tare. Suna komi tare, har ma a wajen neman abinci.

Zomo na da wayo kwarai. Yana tara abinci da  yawa fiye da kura.

Ita ko wannan kura, ragguwa ce, kuma tana son cin abinci kwarai. Koda yake yanayin farautarsu ya banbanta, sun hada abincinsu tare.

Zomo yana amfani da hikimarsa wajen neman abinci da sauri. Kuma ya kan ci kafin ya kawo sauran a wurin da kura take.

A  lokacin fari, yana da wuya  su biyun su tara isasshen abinci da kansu.

Sai kura ta bar neman abinci. Ta dogara akan dan abinda Zomo ya samo ya kawo gida. Wannan yasa Zomon nan ya ji yunwa da bakin ciki. A lokacin da zomo ya dawo babu abinci, sai taji jikinta yayi sanyi.

To amma kuran nan bata nuna alamar zata canza daga halinta na dogaro akan dan abinda Zomon nan za ya tara masu. Rayuwa ta zamo mai wuya saboda Zomo baya iya ciyar da su. Don haka sai Zomon nan ya kuduri ya nemo hanyar rabuwa da wanna kura.

Wata rana kura ta farka da sassafe. Sai suka fara shawarar yadda zasu rayu.

Tattaunawarsu bata kare ba saboda banbancin ra'ayoyi. Kuran nan tace bata iya samo komai saboda bata iya gudu sosai kamar zomo. Saboda haka zata zauna tayi aikin gida.

Da yamma Zomo na farauta, sai yaga danyun 'ya'yan ruman. Ya zauna dan shirya yadda zai kwashe su ya kai gida. Abin da wuya saboda gonar na da shinge.

Tare da sa himma, Zomo ya kai  gabishiyar. Ya hau ya debo masu yawa. Ya ci kuma ya tattara sauran ya sa a kwando, ya dauka. Sai yaji gajiya saboda ya cika cikinsa sosai. Sai yace bari in dan huta,  kawai barci ya dauke shi. Sai ga mai gona ya rutsa shi ya daure shi da igiya ya tabbatar baya iya gudu.

Igiyar na da tsayi kwarai, zomo ya ta ja har yakai inda kura take. Yace mata akwai wata liyafa shi yasa aka daure ni da igiya mai tsawo don kar in bata hanya.

Sai sakaran kuran ya kwance zomon nan ya daure kanshi, ya yi ta bin igiyar har ya tarad da mai gonar a fusace yana jiran isowarsa yana rike da wata shareriyar wuka. Aka yanke kuranan take, aka ba karnukan mai gona suka cinye, sannan aka yi mutum-mutumi da fatar kuran.

------------------------------------------------------------



Kullum da safe suna tashi su karya kuma su gaida I'yayensu.

Habu da lami sun shirya tafiya makaranta.

Habu da lami sukan tafi makaranta akan lokaci.

Suna bada kulawa wurin karatun su.

A gida sukan yi bitar aikin da sukayi a makaranta.

------------------------------------------------------------



Gata nan gata nanku. wani Kunkuru ne mai aiki tuƙuru, ya daɗe yana tattalin 'yan kuɗinsa.

Bayan ya ajiye aiki, sai ya ga yana da makudan kudi.

Don haka sai ya yanke shawarar sayen babbar gona, ya riƙa nomawa.

Labarin kunkuru na neman gona ya saya, ya cika karkarar.

Zomo na jin labarin kunkuru na son sayen gona, sai ya tafi wajen kunkurun ya ce zai taimaka masa.

Sai ya kai kunkuru wata makekiyar gona ya nuna masa da cewa tasa ce.

Kunkuru ya ga gona ta yi masa, don haka aka yi ciniki tsakaninsa da Zomo, ya kuma biya.

Gari na wayewa sai kunkuru ya gayyaci abokansa don a fara shuka a gonar.

Isar su ke da wuya sai suka iske ruwa ya shafe filin. Sai abokan suka tuntsire da dariya suna ce masa,ina filin naka?

Ganin haka sai Kunkuru ya fahimci zomo ya cuce shi, ashe ya sayar masa da gaɓar kogi ne ba filin gona ba.

Tashin kunkure ke da wuya, sai ya wuce wurin alƙali, wato giwa ya kai ƙara. Da jin koken kunkuru, sai ta umurci zaki da ya kamo zomo.

Zomo na jin zaki ya dumfaro gidansa, sai ya fito ya tarbi zakin da murna yana cewa, sauri nake yi don zan je mu kori kerkecinn da suka shigo gari.

Sai zomo ya bi gari yana kuka irin na kerkeci, don haka zaki ya tsorata ya ruga a guje.

Daga nan sai zomo ya yi gaba da kuɗin Kunkuru. Shi kuwa kunkuru 'yan uwa da abokan arziki suka taimaka masa da wata gonar.

------------------------------------------------------------



Fartanyarsa gajera sosai.

Ƙofar gidansa gajeriya ce sosai.

Gadonsa ɗan ƙarami sosai.

Kekensa ɗan ƙarami sosai.

Wannan mutum yana da tsawo sosai.

Ya yi kotar fartanya mai tsawo.

Ya yi ƙofar gaidansa mai tsawo.

Ya yi gado mai tsawo.

Ya sayi keke mai tsawo sosai.

Ya zauna kan kujera mai tsawo sosai. Kuma ya ci abinci da cokali mai tsawo.

Ya bar gidansa ya koma cikin babban daji, ya zauna tsawon lokaci.

------------------------------------------------------------



Wata rana Gizo ya tashi ba shi da abinci, kuma bashi da kuɗin da zai sayi abincin.

Gizo ya ɗauki laujen sa  ya tafi daji ya yanko ciyawa, domin ya kai kasuwa ya sayar.

Gizo ya isa daji, ya fara yankar ciyawa. Har ya tara mai yawa ya ɗaure.

Gizo ya yi ƙoƙarin ɗaukar ciyawar amma  ya kasa, sai ya ce "bari in huta."

Bayan ya huta sai ya koma yanko wata ciyawar ya ƙara.

A karo na uku, Gizo ya koma ƙara wata ciyawar  a kan ta da.

Da ya gagara ɗauka, sai  yace" shi ke nan na huta, bari in tafi gida duk wanda yake so ya saya."

Sai ya koma inuwar wata bishiya yai kwanciyarsa.

Jimawa kaɗan, sai ga wani garken awaki, suna ganin wannan ciyawa sai suka hau kanta,
Su ka yi ta ci har sai da su ka cinye ta.

Lokacin da awaki suka juya za su tafi, sai gizo ya ce wa awakin, ku shaidawa uban gidan ku, 
ina nan ina jiransa ya kawo min kuɗin ciyawar da kuka cinye min.

Gizo ya na ta jira har dare ya yi.

Sai ya ce," Bari in tafi gida, ƙila mai awakin nan ya na can kofar gidana ya na jirana."

------------------------------------------------------------



Biri ya haɗu da Kada a bakin tafki.

Biri ya tambayi Kada a ina ka ke da zama? Sai kada ya ce, "A cikin tafki."

shima kada ya tambayi biri, "Kai kuma a ina kake zaune?"

"Ka iya ninƙaya kuwa?" Kada ya tambayi biri.

Biri ya amsa, "Ban iya ba." Sai kada ya ce, "Zan koya maka."

Kada ya ce, "Yanzu mun zama abokai." Kada ka ji tsoro na.

Kawu na ba shi da lafiya. Yana buƙatar cin nama.

Biri ya tsorata. Kada zai cinye shi ne?

Biri ya na ƙoƙarin kuɓuta daga Kada.

Can sai wata dabara ta zo wa biri.

Biri ya yi alƙawarin, bayar da zuciyarsa ga Kada.

Biri ya ce, "Zuciya ta tana tudu a kan bishiya."

"Za ka ɗauko min zuciyar ka?" Kada ya tambayi biri.

Sai Kada ya yi ninƙaya ya koma tudu. Biri ya ruga.

Kada yace, "Kai ba abokina ba ne kayi ƙarya!"

Biri ya ce, "Mu ba abokai ba ne. Kana so ka cinye ni!"

------------------------------------------------------------



Anyi wa su yara da baban su babbar su ta mutu babban su ne ya ke kula da su

Suna taimaka wa babansu zuwa wajen gona sabuda shi ba shi da karfi

Wataran sai suna cikin tafiya sai ga biri ya zo zai kwace musu kwandon so

Sai ya zauna birin ya cinye musu abin cin su

Bayan sun dawo gida sai babansu yace ina kwadan su kace biri ne ya kwace sai kar ku kara barin shi ya kwace muku

Washe gari suna cikin han yarsu ta tafiya gona sai ga birin nan ya fito sai suka tsorata

Sai birin yana kukarin kwacewa suma suna ja

Sai ga kare nan sai ya tai maka musu

------------------------------------------------------------



Ina son yin wasa da abokina Chuma.

Mu abokanan kirki ne.

Duk sanda aka aiki ɗaya daga cikinmu, tare muke zuwa.

Wata rana, sai kakata ta aike ni shago don na siyo gishiri da man girki.

Sai muka tafi tare da Chuma.

Muna cikin tafiya, sai muka ga abokanmu suna buga ƙwallon ƙafa.

"Kai! Кwallon ƙafa!" Na faɗa.

Ni ma ina son na yi wasan.

Sai na ce da Chuma, "Mu tambaye su ko za mu iya yin wasan tare. Don ni ina son ƙwallon ƙafa sosai."

Sai Chuma ya ce, "Mu fara zuwa shagon, sannan sai mu dawo mu yi wasan."

Amma sai na ce, "Mu fara yin wasan! Don kaka ba za ta bar mu mu dawo ba."

Sai muka shiga abokanmu don yin wasan. Ni ne mai tsaron raga.

Turakun ragar an yi su da manyan duwatsu guda biyu.

Na yi ƙoƙari matuƙa wajen kama ƙwallon.

Don haka abokaina ba su samu damar zura ƙwallo ko ɗaya ba.

Muka yi ta wasa har sai da filin ya cika da yashi.

Sannan sai muka tafi shagon, amma kuɗin kaka sun ɓata! Sai na fara kuka.

Sai Chuma ya daka min tsawa, "Ka daina kuka, ai kai ne ka ce a fara yin wasan da farko."

Sai muka koma gida babu gishiri babu man girki.

Ga shi mun yi datti sosai, hankalinmu ya tashi.

Kaka ta fusata san da muka koma gida.

Abin da ta fara tambaya shi ne, "Ina kuka shiga duk tsawon wannan lokacin?"

A dole muka faɗa mata gaskiya.

Sai ta gargaɗe mu cewa, "Kar ku ƙara zuwa wasa ba tare da izini ba."

Sai muka tafi domin bai wa agwagi abinci.

Daga baya kuma muka wanke jikinmu.

------------------------------------------------------------



Kalli dabbobin.

Saniya na cewa, "Maoo."

Akuya na cewa, "Meah, meah."

Doki na cewa, "Niihii."

Alade na yin, "Gurnani."

Kaza na yin, "Kyarkyara."

Kare na cewa, "Wan- wan."

Manomin ya ce, "Shhh!"

------------------------------------------------------------



An dauki lokaci ana tsamanin saukar ruwa sama, don haka jama'a  suka taru a kofar gidan Liman don a fita rokon ruwa.

Yayin da Liman ya fito ya roki Allah ya ba da damina mai albarka, da kuma fatan samun amfani gona mai kyau.

Washegari yara na wasa a waje,sai gagarimin hadari ya taso daga gabas, da alamun za a samu ruwa.

Ganin cewa an yi rokon ruwa, ga shi kuma hadarin ya hadu sosai don haka mahaifiyar yaran ta ce, su shigo gida.

Daga nan sai aka tsuge da ruwa

Mun yi farin cikin samun ruwan farko, sai dai murna ta koma ciki, don ruwan ya dade bai tsagaita ba.

Ruwa ya malale koina, har ya tafi da gadar da ta hada kauyenmu  da cikin birni.

Gyara ya zamo anoba a gare mu,domin ruwa ya mamaye gidaje da dama.

Jama'ar  karkararmu sun shiga damuwa,kasancewar ruwan ya shafe gonaki da gidajensu, ga shi uwa uba ma gadar garin ta rushe.

Wani abin ban tsoro kuma sai ga Kada na iyo a saman ruwa, wannan ya sa jama'a suka kidime gaba daya.

Don haka duk wata harka ta tsaya, yara  ba damar zuwa makaranta, sakamakon yadda ruwan ya mamaye koina

Wannan annoba ta haifar da damuwa ga  limami tare da al'ummar garin.

------------------------------------------------------------



A cikin daji, wata rana lokacin ana yin mugun zafi.

Ƴar Tururuwar ta yi kwanaki da kwanaki ba ta samu ruwan sha ba.

"Ina bukatar ɗashin ruwa ko da wanda ya faɗo ne daga kunnen icce."

Ba bu ko bazara.

"Idan ban sha ruwa ba za ni iya mutuwa," ƴar Tururuwar ta faɗa. 

"Ya kamata in tafi tabkin nan, da na ji labarin shi."

"Wanan tabkin yana iya tafiya da ke," wani tsofon Kurege ya yi mata kashedi.

Sai dai wannan ƴar Tururuwar ta ji ƙishirwa ƙwarai. 

"Idan ban sha ruwa ba za ni iya mutuwa."

Ƴar Tururuwa ta tafi neman tabkin.

Cikin ciyawa kuma ƙalƙashin reshinen itace busasu.

Har lokacin da ta ji kukan ruwan tabkin.

Ƴar Tururuwa ka ƙwalga sanyayen ruwan tabki.

Tana ta jin daɗi ba ta gani ba ruwan tabki suna bori.

Ƴar Tururuwa ta yi, ta yi ta kama ɗan reshen iccen da yake saman ruwan. 

Amma ruwan sun tafi da ita.

"Ku taimake ni. Don Allah ku cece ni."

"Hawo da sauri," in ji Habjiya, da ta riƙe da wani reshen icce ga bakinta.



"Ba za ni tafiya ba har sai na yi ma Habjiyar nan godiya. Za ni jira har lokacin da ta dawo shan ruwa."

Tana cikin jira, wata rana sai ƴan samari biyu riƙe da kaushun harbi suka zo bakin tabkin.

"Akwai wata babar Habjiya da take zuwa wurin ga shan ruwa," ɗaya daga cikin samarin ya faɗa. "Sai mun same ta don mu yi tuwon dare da ita."



"Ba za ni barin ƴan samarin nan ba su kashe wanan Habjiyar ba. Amma kuma ni ƙaramci ya yi mini yawa,  to yaya za ni yi?"

A wanan lokacin ne, Habjiyar ta sabko daga saman icce don ta sha ruwa.



Sai ƴar Tururuwar ta samu wata dubara.

Ta hawo saman ɗaya daga cikin samarin, ta cije shi da ƙarfi.

Ɗan sarmayin ya buga tsalo. "Wash!" yana kuwa.

Habjiyar ta ji tsoro kuma ta fira ta koma wani wuri.

Ta haka ne ƴar Tururuwa da gode ma Habjiyar da ta cece ta.

------------------------------------------------------------



Wata rana an aiki Musa, Garba da Kande wajen tsinto itacen girki a daji. Dajin ya na da haɗari. Kakarsu ta gargaɗesu kar su yi wasa wajen ɗebo itacen.

Dajin ya na da nisa sosai daga gidansu. Mahaifiyarsu ta kan je da su dajin, amma ranar ta je kasuwa sayen kayan lambu.

Da suka je dajin ba su dawo da wuri ba. Babbarsu ta dawo ta damu da ba ta gansu ba. Saboda haɗarin dajin mutane su na maganarsa. Dajin cike yake da macizai masu haɗiye mutane da Awaki.

Lokacin da za su bar gida an gargaɗesu da kada su shiga cikin dajin sosai. Amma Kande da yake ba ta jin magana ta yanke shawarar shiga ciki sosai. Ta shawarci 'yan'uwanta su shiga tare amma suka ƙi. Ta faɗa musu ta ga itace mai yawa a karan farko da ta je, amma suka ƙi.

Kande ta kan yi abinda aka hanata kowane lokaci. Lokacin da ta ke neman itace sai ta haɗu da wani mutum da ke zaune cikin dajin ya ce mata zai nuna mata inda za ta sami itace mai yawa. Ta kira 'yan'uwanta su tafi tare, sai suka tunatar da ita cewa an gargaɗesu cewa "kar su yiwa kowa magana a cikin daji" amma kawai ta yanke shawarar tafiya.

Musa da Garba sun ɗaure itacensu, sun jira 'yar'uwarsu har sun gaji, amma ba ta zo ba; sai suka tafi suka barta. Lokacin da suka isa gida sai mahaifiyarsu ta tambaye su "Ina Kande"? Suka ce ba su san inda take ba. Maharbi ya ɗauki Kande zuwa gidansa yace ta kwana, gobe ya kaita gida saboda dare ya yi. Mutumin nan ya na zaune a cikin wani kogo tare da namun daji, Kande ta razana matuƙa amma haka ta kwana.

Tsakar dare sai Maharbi ya canja halittarsa, ƙafafuwansa dogaye da yatsu da yawa, kansa ya zamo babba da manyan idanuwa, ƙafafuwansa kamar na giwa. Sai Kande ta ƙara tsorata ta na so ta gudu da safe. Sai ta tuna cewa 'yan'uwanta sun gargaɗeta.

Mahaifiyarta ta ɗauki fitila ta tafi nemanta. Ta shiga cikin daji ta na kiran sunanta tana dubawa amma ba ta sameta ba. Kande ta yi ta yunƙurin gudowa amma Maharbi ya ce "Zai bar ta ne ta tafi kawai idan ta faɗi sunansa". A kullum Kande ta saurara ko mutumin nan zai fadi sunansa. Wata rana bayan ya sha giya sai ya ambaci sunansa "Agagasheshili" sunan ya yiwa Kande tsawo da ba za ta iya faɗarsa ba.

Kullum ta na kuka saboda ta na son tafiya gida amma ta kasa fadar sunan yadda yake daidai. Wata rana Ogre ya same ta tana kuka kuma ya tambaye ta "Mene ne dalilin kukanta"?  Ta ce ta yi ta fadi sunan amma ba za iya fada ba. Lokacin da ya lura ta na ƙoƙarin faƙar sunansa sai ya canja zuwa maciji.

Maciji ya fara magana cewa ba wanda ya san sunansa. Kande ta ji tsoro sai ta fara gudu ba ta yi nisa ba aka haɗiye ta da rai. Danginta suka duba ko ina ba su ganta ba.'Yan'uwanta aka bar su cikin damuwa kamar yadda suke ƙaunarta. Cikin nadama suka ce za su bi umarni.

------------------------------------------------------------



Gatarinshi ƙarami ne ƙwarai.

Ƙofar ɗakinshi ta yi ƙasa ƙwarai.

Gadonshi ya yi gajerta ƙwarai.

Kekenshi ƙarami ne ƙwarai.

Wannan mutumen babban ne ƙwarai.

Ya ƙera wata babbar ƙota ta gatarinshi.

Ya ƙara girman ƙofarshi.

Ya ƙera wani babban gado.

Ya sayi wani keke mai tsawo.

Ya zamna saman wata babbar kujera. Kuma ya ci abinci da wata babbar koshiya

Ya bar gidanshi kuma ya koma cikin babban kurmi. Ya yi ruyuwarshi tsawon shekaru da dama.

------------------------------------------------------------



A zamanin da, kura da gizo sun zauna a gida ɗaya. Kowannensu yana fita neman abinci da safe sai dare zai dawo.

Duk san da gizo ya fita yakan dawo da abinci mai yawa, amma ita kuwa kura, takan dawo babu komai.

Rannan bayan sun dawo,sai kura ta roki gizo ya taimaka mata da abincin dare. Sai gizo ya bata abinci ta ci ta ƙoshi.

Sai kura ta ce, "Don Allah a ina kake samo abinci haka ? Don ni ma na dinga bin ka."

Sai gizo ya ce, "Ke ba ɗa ki iya jurewa ba. Kawai ki bari ɗan dinga san miki."

Kura ta dage cewa ɗa ta iya. Da gari ya waye, sai gizo ya tashi ya tarar kura ta shirya tsaf tana jiran sa ya tashi su tafi.

Sai suka yi doguwar tafiya kafin suka tarar fa woni ƙaton gida. Sai gizo ya ce, "Balan." Sai ƙofar gidan ta buɗe. 

Suna shiga, gizo ya ce, "Zargagum-gum." Sai ƙofar ta rufe. Sai ga kayan abinci iri-iri. Suka ɗiba da yawa sanan suka tafi.

Da suka dawo sai kura ta ce, "Ka bari daga yau ni zan dinga zuwa ɗibo mana abinci, kai kuma ka zanna ka dinga dafa mana mu shi."

Gizo ya amince, amma ya gargaɗi kura da ta Kula sosai domin gidan na wani dodo ne mai iya dawowa a kodayaushe.

Da Kura ta zo gidan dodo washegari, sei ta ce, "Bilan," ƙofa ta buɗe. Ta shiga ta ce, "Zargagum-gum," ƙofa rufe.

Ta ɗibo kayan abinci a buhu amma day ta zo fita, sai ta manta me ake faɗa ƙofa ta buɗe. Ta na cewa zargagum-gum ƙofar na ƙara rufewa.

Da Kura ta rasa hanyar fita, hankslin ya tashi tana kuka. Can da yamma ga dodo ya dawo ya samu kura a tsungune.

Ya ce, "Yawwa yau na kamo mai yi min sata. Zan dafa ki na cinye ki." Kura ta ƙara fashewa da kuka tana roƙon sa ya yi haƙuri.

Kura ta yi wa dodo alƙawari ba za ta sake yin sata ba idan ya ƙyale ta. Dodo ya ƙyale ta tafi bai mata komai ba.

Da ta je gida sai ta ba wa gizo labari duk abin da ya faru. Sai gizo ya tsorata. Daga nan sun daina satar kayan woni Kuma.

------------------------------------------------------------



Wata rana da makaho da mai ido sun je satar mangwaro

Da suka hau bishiyar, sai ga mai gonar. Mai idon ya ce "ga mai gona"

Sai suka sauka daga bishiyar suka ruga da gudu.

Sai mai idon ya ce "a tare, a tare, makaho zai faɗa ruwa!

Wajen kuma babu ruwa, amma makahon ya toshe kunne da hanci

Sai ya buga nutso, ya buga fuska a kwalta, ya kurkurje a fuska

Sai ya ce "wayyo, Allah, na mutu na lalace."

------------------------------------------------------------



A wani lokaci ,wata da Rana a duniya suke rayuwa,Rana Yana da aboki wato ruwa ,sai Rana ya gayyaci abokinshi wato ruwa

Sai wata da ahalinsa suka zo gidan rana da wata suka fara cike gidansu ko ina ruwane sai ruwa yace WA wata da Rana "haka ya Isa ne ko a'a" sai Rana yace ku cigaba da shugowa

Sai rana tace ya Isa haka nagode

Daga nan Rana da wata suka koma 
Rayuwa a sama

------------------------------------------------------------



A wani lokaci an yi wata kada da take rayuwa a kogi tare da 'ya'yanta.

Kadar ta koyawa 'ya'yanta kada su aminta da ɗan'adam.

Saboda mutane suna da ƙwaƙwalwa.

Wata rana, wani mutum ya tsallaka kogi.

Mutumin nan ya zo tsakiyar kogin sai ya gamu da kada, ta kai masa hari.

Lokacin da kadar ta kusa kashe shi, sai ta tuna abin da babanta ya gaya mata.

Yana yawan gaya mata cewa mutane suna da ƙwaƙwalwa.

Mutumin ya yi mata alƙawarin zai kawo mata ƙwaƙwalen mutane.

Saboda haka sai kadar ta sake shi.

Kadar da 'ya'yanta suna nan suna jira a bakin kogi domin su karɓi waɗannan ƙwaƙwalen.

Kadojin suna jin haushi har yau, domin ba su samu abin da aka yi musu alƙawari ba na ƙwaƙwalwar mutum.

------------------------------------------------------------



An yi wasu ƙannu biyu da ake kira Halima da Fatuma. Uwayensu sun rasu. Ƴan matan biyu suna rayuwa a wani yanki mai hamada. Ba ruwan sama,  ba cimaka. Kowa yake son abincin,  sai ya yi tafiya mai nisan gaske.

Halima yarin ce ma ɗa'a,  lafiya da kuma kirki. Ƙanwarta Fatuma tana son rayuwa kuma ba ta jin gargaɗi. Ba ta kula da sauran mutane kuma ba ta darajjanta su.

Wata rana,  ƙannuwan biyu sun tashi daga barci,  kuma sun fiskanci cewa babu abinci ko kaɗan. Sai suka yi niyyar tafiya neman abincin. Halima da Fatuma sun ɗauki hanya dabam-dabam.

Lokacin nan,  wata tsofuwa da ake kira Amina tana rayuwa kusa da gari. Tana da ƙoƙarin temakawa don tana da arzika. Sai dai Amina tana da kuturta,  kuma duk jikinta ƙuraje ne.

Fatuma ta haɗu da wannan tsofuyar,  da ta kiraye ta "Ɗiyata,  kina lafiya? Daga ina kike? Ina za ki?"

Fatuma ta amsa duk tambayoyin. Bayan haka, sai tsofuwar matar ta ce,  "Maida ni gidana,  kuma zan gaya miki abin da za ki yi." Fatuma ta wulaƙanta tsofuyar. Ta ce mata: "Na fi son in mutu da taɓa wannan ƙurajen naki."

Tsofuwar ba ta ce komi kuma ta mata fatan ta sabka lafiya.

Fatuma ta yi ta tafiya har sai da ta zo wani wuri na mamaki. Wurin akwa shanshani,  macizai,  kai da duk wani ƙwari. Fatuma ta gaji,  kuma ga yunwa saboda ba ta ci komi ba. Ko da ta zamna ta futa,  sai ƙwarin suka fito suka cinye ta.

Bisan hanyarta,  Halima ita ma ta haɗu da tsofuwar. Ta yi farin cikin ganin Amina,  saboda ita ce mutum ta farko da ta haɗu da ita cikin wannan bulaguron. Tsofuwar ta kiranyo ta kuma ta muta tambayoyi kamar yadda ta yi ma ƴar uwarta.

Fatuma ta yarda ta maida tsofuwar gidanta. "Kin yi aikin da mutane da yawa suka guje ma," in ji tsofuwar. Sai ta ba ma Fatuma wata sanda kuma ta ce mata ta koma gida,  can za ta iske duk abin da take so.

Fatuma ta gode ma tsofuwar sosai kuma ta yi gaugawa ta koma gida. Ta tarda a gidan,  ɗaki cike da kaya da abincin. Ta zamanto it ace ma arzikin garin.

Amma ta yi ta kuka da rishin ƙanwarta kuma ta ce,  "wandan bai jin gargaɗi zai gamu da mugun abu."

------------------------------------------------------------



A wani lokaci mai tsawo, dukkanin dabbobi sukan yi magana.

Sauro da mahaifiyarsa sun rayu a wani gida.

Kodayaushe mahaifiyar sauron takan bar shi a gida in za ta je nemo abinci.

Wata rana, bayan mahaifiyar ta fita, shi kuwa ɗan ƙaramin sauron yana son fita waje.

Bayan mahaifiyar ta dawo, sai tarar cewa ɗanta ya fita waje.

Ta yi matuƙar damuwa, saboda shi kaɗai ya fita.

Kwatsam sai ga ƙaramin sauron ya dawo gida.

Cikin matuƙar farin ciki, sai ya ce baba, mutane suna murna in sun gan ni. 

Har suna ma min tafi idan na tashi cikin sauri na wuce ta wajensu.

Mamar sai ta ji tsoro ta ce.

"Ka ce mutane suna murna kuma suna yi maka tafi ko?"

Mahaifiyar sai ta yi masa bayani ta ce, "Ba wai murnan ganin ka suke ba." Kawai so suke su muttsuke ka. 

Ta gargaɗe shi ta ce, "Mutane ba sa taɓa murna da ganin sauro."

------------------------------------------------------------



Ramatu tana rayuwa tare da uwayenta har lokacin da suka rasu tana da shekaru goma.

Sai wata ƴar uwarta Dela, da zumuncinsu yake da nisa ta riƙeta. 

Ko da yake Dela ta tsufa, ta gaji kuma ga talauci, amma tana riƙe da ita da zuciya guda.

Ko da yaushe sai Ramatu ta tafi wajen kabarin mahaifanta ta faɗa masu damuwarta.

Wata rana da tafi ziyarar sai ta samo kyautar wani abu. 

Wata gyaɗanma ce ta musaman, ta isko saman ƙabarin mahaifanta.

Gyaɗanmar ta rera mata wata waƙa mai daɗi kuma da kwantar da hankali. Ramatu ta gano muryar mahaifiyarta. 

Ga yadda maganganun suke:

Ramatu, Ramatu! 
Ɗiyarmu, da muke so! 
Ba ke kaɗai ba ce, ɗiyata! 
Riƙe wanan gyanɗamar, ɗiyata! 
Tafi da ita duk inda zaki tafiya, ɗiyata! 
Za ta kwantar maki da hankali!

Duk inda Ramatu za ta tafiya tana tare da gyanɗamar. 

Sai ta ji kamar mahaifanta suna tare da ita kuma suna kareta.

Wata rana, sai wani hatsari ya samu gyanɗamar ta yin dobo, ta fashe lokacin da Ramatu ta tafi ɗibar ruwa tabki. 

Ran Ramatu ya ɓace matuƙa.

Ramatu ta tattara sakainin gyanɗamar cikin hannuyanta ta fara waƙa:

Babana da inata, ku dubi, gyanɗama ta fashe. Gyanɗamar da kuka bani. Mi za ni yi baba da ina? 
Ku yi mini kirki, kuma ku ƙara aiko mini wata alama Don in gane da kullum kuna tare da ni.

Ramatu ta ji muryar uwarta tana ce mata, "Ɗiyata,  tattare kingin sakainin da ya yi saura. Ɗauki ki ɗebo ruwa kuma ki wanke ƙafafunki. Idan kin ƙare sai ki wanke idanunki." 

Ramatu ta bi umurnin kuma nan da nan, gyandamar da ta fashe sai ta Ramatu daidai.

Ramatu gaba da tafiya da gyanɗamar duk inda za ta tafiya. Duk inda ta wuce sai mutane sufara gulma tsakaninsu, "Mi yake cikin wacen gyanɗamar?" 

Da gyanɗamarta ta dabo Kayanga tana samun duk abin da take bukata.

Da gyanɗamarta ta dabo, Ramatu ta san da mahaifanta suna tsare da ita.

Duk wani shairi baya samun ta.

------------------------------------------------------------



Wata rana Joha zai je kasuwa. Sai ya haɗu da abokinsa

Sai abokin ya tambaya, "Ina zaka Joha?" Joha yace zani kasuwa.

Dan in sayo jaki. Sai abokin yace masa ka ce in Allah yaso ya yarda.

Aa! Ina da kuɗi kuma akwai jakai a kasuwa.

Sai aka sace kuɗin a kasuwar. Joha yace Oo! ba sauran sayen jaki a yau.

Joha yayi nadama rashin faɗin in Allah yaso ya yarda.

------------------------------------------------------------



A wani zamani can baya, anyi wani mutum mai Saniya wai shi Alto. Kullun Alto ya kanyi kiwon saniyar. Ya kan kuma shayar da ita. Amma yana amfani da ƙaramar tukunya ne.

Don haka sai ya je gidan maƙwabcin sa don ya bashi aron babbar tukunya. Maƙwabcin sa  ya bashi aro ya ce masa, "Ai matsalar maƙwabcin ka taka ce."

Bayan wasu yan kwanaki, sai Alto ya je wajen magina tukwane ya sayo wata 'yar qaramar tukunya, ya kai gida. Ya sa ta a cikin babbar tukunyar da aka bashi aro.

Bayan ya saka ƙaramar tukunyar a cikin babbar, sai ya ɗora a kan sa. Ya kai gidan maƙwabcin nan da ya bashi aro.

Alto ya ce masa, "Na dawo maka da tukunyar da na ara, harma ta haihu." Maƙwabcin ya yi murna da jin cewar tukunyar sa ta haihu. Ya yabi Alto matuƙa harma yayi masa adduar Allah ya yi masa albarka.

Bayan kwana biyu, sai Alto ya koma wurin maƙwabcin nan na sa don ya ƙara ara masa babbar tukunyar nan harwayau. Amma fa da mummunar manufa a ran sa.

Mai tukunya ya yi ta jira shiru shiru Alto bai dawo da tukunyar ba. A ƙarshe ya je gidan Alto, "Na zo kan batun tukunya ta."

Alto ya ce wa maƙwabcin nan nasa, "Ayya abokina, tukunyar nan ta rasu." Yanzunnan nake son zuwa in kai ma baƙin labari.

Maƙwabcin nan ya buga tsalle ya yi mamakin wannan al'amari. Cikin fushi ya dakawa Alto tsawa, "Ban taɓa jin inda tukunya ta rasu ba!"

Alto ya amsa masa da cewa, "Haba abokina, yakamata ka yarda duk mai haihuwa wata rana zai iya mutuwa. Ni kaina ina jimamin rashin wannan babbar tukunyar."

Maƙwabcin ya fusata ya kai ƙarar Alto wurin Alƙali. Da Alƙali ya gama sauraron ƙarar. Sai ya ba maitukunyar rashin gaskiya.

"Lokacin da Alto ya zo maka da labarin haihuwar tukunyar ka ai yarda ka yi ba ka yi musu ba. Da ya ce maka duk mai rai inhar zai haihu to zai iya mutuwa, ai haka ne."

Maƙwabcin Alto ya koma gida jikin sa a sanyaye tamkar dodonkoɗi. Alto ya mallake babbar tukunyar ta hanyar yaudara.

------------------------------------------------------------



Yarinya tana tafiya

Tsuntsu yana tashi

Kare yana haushi

Mage tana cikin ɗaki

------------------------------------------------------------



Rana ta na fitowa daga gabas ko wace safiya.
  
 Na kan ji kukan zakara yana chara da asubah.

Rana ta na gangarawa saman gidan Terfa, kafin abincin safe.
  
Na ji kamshin bier da akpupa yana biyo rana ta taga na.

Rana ta na wucewa bayan bishiya a makaranta kafin abincin rana.
  
Sai ta iso bakin kuddudufi a sakiyan filin wasa.

Rana ta kan haye bisa kai na. inuwa na ta kasance gefe na.
  
 Na kan yi wasan inuwa da abokai na.

Inuwa ta kan yi girma, sai ta kakance. Sai mu kan bi ta da gudu.
  

  Inuwa ta kan yi tsayi, sai ta kan gajarce. Sai mu kan bi ta da gudu.

Na kan tsaya, abokai na kan tsaya. Sai mu kan ga inuwan mu sun kauce.
  
Mun kan gaji, sai mu kan koma aji. Baya makaranta, sai mu kan tafi gida.

Rana tayi yawshi.
  
Na kan ga rana tana faduwa a hankali zuwa kudu. Sai na kan ga.
  inuwa na a bango. Lokacin barci yayi.

Rana ta kan fadi bayan gajimarai.
  
  Na kan kwanta a kan gado na, sai na kan yi mafarki rana na tafiya nesa-nesa.

------------------------------------------------------------



Watarana Zomo yana cikin tafiya a gefen kogi.

Ita ma Dorina ta fito shakatawa, kuma ta ci korayen ciyayi.

Dorina ba ta san cewa Zomo na wajen ba, sai ta taka masa kafa. 
  
Zomo ya ji zafi ya fara ihu yana cewa, "Ke Dorina ba ki ga kin taka min kafa ba?"

Sai Dorina ta ba Zomo hakuri ta ce, "Ayya, yi hakuri Zomo, ban gan ka ba ne, ka yafe min."
  
Amma Zomo bai yarda ba, sai ya cigaba da ihu yana cewa, "Ba wani nan, kina sane kika taka ni, kuma za ki gani, watarana sai na rama!"

Daga nan sai Zomo ya tafi wajen Wuta ya ce, "Je ki kona Dorina idan ta fito daga cikin kogi za ta ci ciyawa, domin ta taka ni!" 
  
Sai Wuta ta ce, "Ba damuwa abokina. Zan yi duk yadda ka ce."

Jimawa kadan, Dorina ta fito tana cin ciyawa a nesa da kogi, kwatsam! Sai Wuta ta tashi. Fara yaduwa.
  
Ta fara kona gashin Dorina.

Dorina ta fara kuka, ta ruga a guje ta fada cikin ruwa. Duka gashinta wuta ta kone shi. 
  
Dorina ta cigaba da kuka tana cewa, "Wayyo gashina, gashina ya kone a cikin wuta, shikenan yanzu bani da gashi, wayyo kyakkyawan gashina!"

Zomo ya yi farinciki cewa gashin Dorina ya kone. 
  
Tun daga wannan ranar, Dorina ba ta nisa daga bakin kogi sabo da tsoron wuta.

------------------------------------------------------------



Bunty tana son wasa da kwari.

Da kuma tsuntsaye.

Tana kuma son wasa da jirgin takarda.

Sannan tana son gina gidan kasa.

Idan Bunty ta koma gida, sai mamanta ta ce mata ta je ta yi wanka. 

Amma Bunty ba za ta yi ba.

Sai Bunty tai ta ihu tana cewa, "Na tsani sabulu!"

Watarana sai Bunty tai mafarki da kwayoyin cuta sun zagaye ta suna cizonta.

Kwayoyin cutar su kai ta cizonta, Bunty ta ruga da gudu tana kuka tana neman taimako.

Kwatsam, sai ga katon Sabulu ya zo ya ce, "Kada ki ji tsoro Bunty." Sai ya saka kananan sabulai su je su kori kwayoyin cuta.

Rundunar kananan sabulan nan suka kori kwayoyin cuta gaba dayansu.

Tun daga ranar Bunty take son yin wanka, ta wanke baki, sannan ta tsaftace duka jikinta.

------------------------------------------------------------



A wani gari mai suna Magarya. An yi wani mutum mai suna Bunu.

A garin Magarya, masana labarai suke bada labarai masu ƙayatarwa

Da aka zo kan Bunu, sai ya ce "labarina a kan damisa ne."

Yana faɗin kan labarinsa, sai kowa ya yi shuru ya kuma saurara.

Bunu ya gyara murya ya ce, "Damisa kamar Kyanwa ta ke."

Sai kowa ya ce "Lallai, haka ne".

Kuma ya ce, "Damisa na da tsawon bindi."

Sai masu saurare suka ce. "Ummm, gaskiya ne!"

Lokacin da Bunu ya fahimci ya fara birge jama'a.

Sai ya yi farat kamar ƙwararren mai bada labari, ya ce "Ai lokacin da muke yara, malamin mu ya kai mu bakin rafi ya nuna mana damisa."

Ita damisa tana da ƙaho biyu irin na barewa."

Sai kowa ya ƙyalƙyace da dariya yana yi masa ba'a.

"Bunu maƙaryaci ne, kuma bai san yanda damisa take ba."

Bunu ya gane kuskuren sa sai ya ce, "Daga yau ba zan
sake ba da labarin abinda ban sani ba.

------------------------------------------------------------



A wani lokaci a can baya, anyi wasu yara maza uku da mace ɗaya. Dukansu 'yan ƙauyen Nakwiga ne.

Suna karatu ne a makantar firamare ta Busolwe.

Akan hanyar su ta zuwa  makaranta, sukan ji kukan tsuntsaye.

Wata rana yarannan suka ƙuduri su tsere daga makaranta, sai suka tafi farauta a dajin dake kusa da su.

Sai suka ga wani tsuntsu. Tsuntsun ya fara rera kukansa kamar yana faɗar, "kuna kira na da kalmar ɓatanci, ni ba sakarai ne ba, har sau huɗu."

Ni na gari ne, amman in kuna jin ni sakarai ne, to zan nuna maku ni lallai sakarai ne a nan gaba. Sai yaran suka kama tsuntsun suka tafi da shi gida.

Da suka isa gida sai suka yanke shi suka cinye.

Kashe gari duk sai suka kamu da rashin lafiya. Saboda namanshi na ɗauke da guba.

------------------------------------------------------------



Delu ta kalli yara maza suna wasar qwallon qafa. Ta yi shaawar shiga tayi wasar da su. Ta tambayi Maihorar da 'yan wasar, "Ko zata  iya shiga ayi wasar da ita?"

Maihorar da 'yan wasar ya riqe qugunsa da hannuwansa. "A wannan makarantar, Maza ne kawai aka yarda suyi wasan qwallon qafa." Ya ce.

'Yan mazan suka ce mata, "Ta je tayi wasan qwallon raga." Suka ce, "Qwallon raga na mata ne, qwallon qafa kuwa na maza ne." Wannan ya vata wa Delu rai.

Washe gari, makarantar tana da babban wasa. Maihorar da 'yan wasan ya damu matuqa saboda haziqin xanwasan sa bashi da lafiya, bazai sami dammar yin wasa ba.

Delu ta roqi Maihorar da 'yan wasa cewa, "Don Allah ka bani dama in buga wasan." Maihorarwar, ya rasa abin da zaiyi. Sai ya yanke shawarar sa Delu cikin 'yan wasan.

Wasa ya yi zafi. Duk qungiyoyin basu sa qwallo a raga ba har zuwa hutun rabin lokaci.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Delu ta amshi qwallo. Sai ta ja qwallon zuwa ragar abokan karawar su. Sai Delu ta daki qwllon da karfi sai ta shiga raga.

Taron 'yan kallo sunyi ihu don murna. Tun dag wannan lokaci, aka baiwa 'Yan mata damar yin wasan qwallon qafa a makarantar.

------------------------------------------------------------



Anyi wani dila mai wayo da yake cin tsuntsaye da kaji.

Sai dilan ya sa rawani ya dau carbi zuwa lambu.

Da ya fita farauta, ya yi ta rera waqa ya na cewa da jaki da zakara su sauko suyi mana Kiran sallah asuba ta yi.

Da jin haka, saniya ta ce da zakara sauko abokina kayi mana Kiran sallar asuba, GA limamin ya sa rawani ya dau carbi zuwa masallaci.

Sai zakara ya ce, "Kar Ku yedda da ci. An tabbatar da ci mayaudari ne. Yana cinye ƴaƴan kaji tsuntsaye."

Sai saniya ta ce da dila, "Akace kai mayaudati mai cin ƴaƴan mutane Ko?"

"Na daina cin tsuntsaye da kaji tun da dadewa. Na Koma cin kankana, lemu, ayaba da sauransu," Dila ta amsa.

Sai saniya ta ce da zakara, "Ya fa deina cin ƴaƴan tsuntsaye da kaji, ya Koma cin kayan marmari. Wato kankana, lemu, ayaba, abarba da sauransu."

Sai zakara ya ce, "Ni babzan yarda ba, idan ku kun yarda zanyi kiran sallah akan bishiya dan mu yi sallar asuba."

Sai zakara da tsuntsaye suka cewa saniya, "Wannan shi ake kira da wayon a ci shi ya sa aka kori kare daga gindin ɗinya."

------------------------------------------------------------



Ko da yaushe, Damisa na qoqari ta kama Barewa.

kuma Barewa  na tsere ma Damisa ko da yaushe.

Wata rana, Damisa ta kira Barewa, "mu zama abokai. Abin da ki ke ci ba na ci. Babu wani abu da zai sa mu gaba."

Barewa ta yarda. Don haka Damisa ta ce, "Bari mu ranste don mu zama abokai. Idan kowane xayan mu ya karya rantsuwar, yaro zai mutu."

Su ka  rantsai
  don zama abokai. Da dare, Barewa tayi bacci a gindin bishiya. Damisa tayi bacci
  a kan rassan a sama.

Ba da daxewa Barewa ta yi qiba. Damisa ta sirance.

Damisa ta yi qwaxayin cin Barewa. Ta fada ma kanta, “ban damu da rantsuwar ba. Ba ni da yara!”

Damisa ta yi tselle zuwa kasa  don kama Barewa. Amma ta maqale tsakanin
  rassan biyu.

Barewa ta gigice. Ta yi tsalle ta fashe da kuka, “Beh! Beh!”

Damisa ta yi roqo, “Aboki na, taimake
  ni. Mun yarda cewa duk
  wanda ya karya rantsuwar mu ta zama abokai, zai rasa yaro.”

Barewa ta amsa, “ ya kamata mahaifin ki ce
  ta yi rantsuwar. Yanzu ta zama na ki!”

------------------------------------------------------------



Kyanwa nawa ne? Babu kyanwa ko guda. Ba kyanwa.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa daya ce. Baƙar kyanwa na iya cin jan nama.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa biyu ne. Fara da ruwan toka. Farar kyanwa da ruwan toka suke wasa a cikin furanni da kuma kan dabe.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa uku. Toka-toka, madara-madara, ɗabbare-ɗabbare. Suna wasa sama da ƙasan  bango.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa huɗu. Kyanwa huɗu abokan Ali ne.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa biyar. Kyanwa biyar na ta wasan kai-kawo a ɗakin hutawa. Ina son haka.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa shida. Kyanwa shida suna iya zama tare su kalli fim.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa bakwai. Kyanwa bakwai na wasa a tsakar gida.

Kyanwa nawa ne? Kyanwa takwas. Kyanwa basa son karnuka.

'Yar kyanwa ta maƙale a kan bishiya! Ali ya ce, "Zan ceto ki."

"Inna ko mu ajiye shi? saura daya tal." Kyanwa nawa ne? Inna tace kyanwa tara sun yi yawa.

------------------------------------------------------------



Wata rana da farar safiya,  kakar Idi ta yi kiran shi,  "Idi,  don Allah,  kana iya kai ma ma'aifanka wannan ƙwan? Suna son su yi wani babban biskiti na auren ƙanwarka."

Lokacin da yake zuwa gida ma'aifan nashi,  Idi ya gamu da wasu samari biyu suna cirar ƴaƴan itace. Ɗaya daga cikin yaran ya ɗauki ƙwai ɗaya kuma ya jefa saman iccen. Ƙwai ya fashe.

"Mi ka yi?" in ji Idi. "Wannan ƙwan na yin biskiti ne,  biskitin auren ƙanwata. Mi ƙanwar tawa za ta ce idan babu biskitin auren ta?"

Samari ba su ji daɗin wannan wasan da suka yi ma Idi. "Babu yadda za mi yi don yin biskiti,  amma ga wannan sandar ka kai ma ƙanwarka." In iji ɗaya daga cikin su. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

Bisan hanya,  ya tarda mutane biyu suna gina wani gida. "Muna iya amfani da wannan sandar taka mai ƙwari?" in ji ɗaya daga cikin mutanen biyu. Amma da yake sandar ba ta da ƙwari sosai,  sai ta kariye.

"Mi kuka yi?" in ji Idi. "Wannan sandar kyauta ce aka ma ƙanwata. Masu ciran ɗiyan itace suka ba ni don sun fasa ƙwan da za yi biskitin auren ƙanwata. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu ba ƙwan,  ba biskitin kuma babu kyauta ko ɗaya." Mi ƙanwar tawa za ta ce.

Maginan ba su ji daɗi ba da suka karya sandar. "Ba mu san abin za mu yi ba, amma ga ciyawa kaɗan ka kai ma ƙanwarka," in ji ɗaya daga cikinsu. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

Bisan hanya,  Idi ya tarda wani makiyayi da saniya. "Wannan ciyawar sai ta yi daɗi,  ko ka ba ni kaɗan?" in ji saniyar. Sai da yake ciyawar tana daɗi,  saniyar ta cinye duka.

"Mi kika yi?" in ji Idi. "Wannan ciyawar,  kyauta ce aka ma ƙanwata. Magina sun ba ni ciyawar don su karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu biskitin,  ba kuma kyauta ɗaya. Mi ƙanwar tawa za tace?"

Saniya ba ta ji daɗi ba da ta cinye ciyawar. Makiyayin ya ɗauki niyyar bada saniya don tar aka di kuma ta zama kyauta ga ƙwanwarshi. Idi ya ci gaba bisan hanyarashi.

Sai dai lokacin da za a yanka saniyar,  sai ta gudu ta koma ga mai ita. Idi kuma ya ɓadda sawunta. Ko da ya zo wajen auren ƙanwar tashi,  mutane sun yi abincin.

"Mi za ni yi?" in ji Idi. "Saniyar da ta gudu,  kyauta ce kambacin ciyawar da magina suka ba ni. Magina sun ba ni ciyawar don sun karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu saniyar,  ba biskitin,  ba kuma kyauta ɗaya."

Ƙanwar ta Idi ta yi tunani kuma ta ce: "Idi ƙanena,  ban damu da wannan kyautar. Ban damu da biskitin ba. Yau ranar murna ce,  ina farin ciki. Sanya tufafinka na salla ka zo mu raya wannan ranar!" Sai idi ya yi hakan.

------------------------------------------------------------



Musa yaro ne mai ƙoƙari, sai dai fitinanne ne. Yana zaune da mahaifanshi a ƙauyen kagadama.

Musa yaro ne mai zaluntar yara 'yan uwanshi. Wani lokaci ma har dabbobi ma in ya gani ko a gida ko hanya sai ya basu wahala.

Rannan akan hanyar sa ta dawowa daga makaranta, sai ya tsinto kyanwa. Yana ganin ta sai ya sa hannu ya ɗauke ta, ya kai ta gidan su.

Baban shi yace, kai musa? Ka mayar da kyanwar nan inda ka ɗauko ta, ka daina bata wahala.

Musa bai ji maganar baban shi ba sai ya kulle kyanwar a akurki bai bata abinci.

Wata rana yana kwance a ɗaki da daddare, sai ya ga kyanwar nan ta zama ƙatuwa, ta nufo shi da bakin ta a buɗe, hakoranta zako-zako za ta haɗiye shi.

Ta fara daga kafafun sa, suka shige cikin bakin ta gaba ɗaya, sai musa ya farka daga bacci ashe Mafarki yake!

Gari na waye wa, musa ya mayar da ita inda ya ɗauko ta, daga nan yayi alƙawarin gyara halayen sa.

------------------------------------------------------------



A wani babban gari me suna Rici, akwai wani ƙauye mai suna Gimi, 'yan ƙauyen sun kasance sunfi ba wa talla muhimmanci,

a ƙauyen akwai wani mutum mai suna malam Musa. Ya kasance ma aikacin gwamnati. malam Musa ya tsaya tsayin daka ganin 'yar sa magajiya tayi karatun zamani.

Bayan shekarun aikinsa na gwamnati sun cika, sai ya koma sana'ar noma. A wata shekara, noman malam Musa bai yi kyau ba, har ya kasance sun rasa abun da zasu ci. 'Yan ƙauyen sukayi ta surutu cewa yakamata ya bar 'yarsa ta fara talla.

Duk sanda magajiya zata tafi makaranta, sai yara su dinga mata dariya. Tun tana kuka har tazo ya daina damun ta.

A kwana a tashi, magajiya ta kammala makarantar gaba da firamare. Rana daya mai shela ya zo sanarwa, cewa: "mai gari yana gayyatar duk wanda ya kammala karatun sakandare, gwamnati za ta ba shi gurbin karatu ƙasar waje".

Magajiya ta samu gurbin karatu a kasar waje amma bata so rabuwa da 'yan uwanta ba musamman iyayenta. Baban ta malam Musa yayi mata nasiha sosai a kan ta dage sossai a karatunta sannan ta zama mai gaskiya da rikon amana.

bayan ta fara karatu sai ta kasance mai kwazo ta fannin likitanci, saboda kwazo, gaskiyar ta da kuma rikon amanar ta aka ba ta aiki ta zama babbar likita

a kowane lokaci tana tuna i me zai kawo ci gaba a qauyen su kamar bunkasa ilimin 'ya'ya mata

bayan wasu shekaru magajiya ta dawo daga kasar waje da arziki mai yawa,nyan qauyen su sukayi nadamar maganganun da sukayi a baya game da ilimin ya mace

iyayen magajiya sun farin cikin ganin yadda yarsu ta zama abar kwantance a qauyen gaba daya.  A karshe magajiya ta yi nasarar bude makaranta a qauyen su domin bunkasa ilimin ya mace.

------------------------------------------------------------



Wata rana da farar safiya, kakar Idi ta yi kiran shi,  "Idi, don Allah, kana iya kai ma mahaifanka wannan ƙwan? Suna son su yi wani babban biskiti na auren ƙanwarka."

Lokacin da yake zuwa gida mahaifan nashi, Idi ya gamu da wasu samari biyu suna cirar ƴaƴan itace. Ɗaya daga cikin yaran ya ɗauki ƙwai ɗaya kuma ya jefa saman iccen. Ƙwan ya fashe.

"Mi ka yi?" in ji Idi. "Wannan ƙwan na yin biskiti ne,  biskitin auren ƙanwata. Mi ƙanwar tawa za ta ce idan babu biskitin aurenta?"

Samari ba su ji daɗin wannan wasan da suka yi ma Idi. "Babu yadda zamu yi don yin biskiti, amma ga wannan sandar ka kai ma ƙanwarka." In ji ɗaya daga cikin su. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

Bisan hanya, ya tarda mutane biyu suna gina wani gida. "Muna iya amfani da wannan sandar taka mai ƙwari?" in ji ɗaya daga cikin mutanen biyu. Amma da yake sandar ba ta da ƙwari sosai, sai ta kariye.

"Mi kuka yi?" in ji Idi. "Wannan sandar kyauta ce aka ma ƙanwata. Masu ciran ɗiyan itace suka ba ni don sun fasa ƙwan da za yi biskitin auren ƙanwata. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu ba ƙwan, ba biskitin kuma babu kyauta ko ɗaya." Mi ƙanwar tawa za ta ce.

Maginan ba su ji daɗi ba da suka karya sandar. "Ba mu san abinda za mu yi ba,  amma ga ciyawa kaɗan ka kai ma ƙanwarka," in ji ɗaya daga cikinsu. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

Bisan hanya, Idi ya tarda wani makiyayi da saniya. "Wannan ciyawar sai ta yi daɗi, ko ka ba ni kaɗan?" in ji saniyar. Sai da yake ciyawar tana da daɗi,  saniyar ta cinye duka.

"Mi kika yi?" in ji Idi. "Wannan ciyawar, kyauta ce aka ma ƙanwata. Magina sun ba ni ciyawar don su karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu biskitin, ba kuma kyauta ko ɗaya. Mi ƙanwar tawa za ta ce?"

Saniya ba ta ji daɗi ba da ta cinye ciyawar. Makiyayin ya ɗauki niyyar bada saniya don ta raka shi kuma ta zama kyauta ga ƙwanwarshi. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

Sai dai lokacin da za a yanka saniyar, sai ta gudu ta koma ga mai ita. Idi kuma ya ɓadda sawunta. Ko da ya zo wajen auren ƙanwar tashi, mutane sun yi abinci.

"Mi za ni yi?" in ji Idi. "Saniyar da ta gudu, kyauta ce kambacin ciyawar da magina suka ba ni. Magina sun ba ni ciyawar don sun karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu saniyar,  ba biskitin, ba kuma kyauta ko ɗaya."

Ƙanwar ta Idi ta yi tunani kuma ta ce: "Idi ƙanena,  ban damu da wannan kyautar. Ban damu da biskitin ba. Yau ranar murna ce, ina farin ciki. Sanya tufafinka na salla ka zo mu raya wannan ranar!" Sai idi ya yi hakan.

------------------------------------------------------------



Kowa ya san da giwa tana da babban hanci.

Amma can dauri, hancin giwa babba ne kuma yana da girma. Hanci ya yi kamar takalmi saman fiskarta.

Wata rana sai giwa ta aifi wani jinjiri mai ƙwanƙwanto.

Jinjirin giwar yana da yawan tamabayoyi ga kowace dabba.

Yana mamakin raƙumin daji.

"Don mi kake da dogon wuya," in ji jinjirin giwar.

Yana mamakin karkandam.

"Don mi ƙafonka yake da tsini?"

Yana mamakin dorina.

"Don mi kike da jan ido?" jinjirin giwar yake tambaya.

Kuma yana mamakin kado.

"Mine ne abincika na dare?"

"Kar ka ƙara faɗin haka!" in ji mahaifiyarshi giwa.

Sai jinjirin ya yi nisa da ita yana susar ido.

Amma da yake hankaka yana da wayo sai ya ce mishi, "Ka biyo ni bakin tabki. A nan kana ganin abin da kado yake ci da dare."

Jinjirin giwar ya bi bayan hankaka har bakin tabki.

Ya ratsa ciyawa kuma ya tsaya bakin tabkin. 

Ya dubi ruwan. Ina kadon yake?

"Ina kwana," in ji wani dutsi a bakin ruwan.

"Lafiya lau," in ji jinjirin giwar. "Ko za ka iya gaya mini abun da kada yake ci da dare?"

"Duƙo in gaya maka," in ji dutsin. "Matso, matso ka ji," Jinjirin giwar ya duƙo, har.

"Wup!" hanci cikin bakin kado.

"Kado, mi kake ci da dare." Hankaka yake faɗi.

Jinjirin giwa ya ja, ya ja tun ƙarfinshi, ya kasa.

Amma kado ya ƙi ya saki.

Jinjirin giwa, ya ja, ya ja, ya ja har "Dum!" ya faɗi bisan bayanshi.

Kado ya ji haushin abincinshi ya kubce mishi.

Jinjirin giwa ya dubi hancinshi.

Bai ga ƙarshen hancin ba.

Hancin ya yi tsawo, kamar ya miƙa shi saman icce ya ciro wani abu.

Ya iya kuma ya shaƙo ruwa masu zafi.

Tun daga shi ne, giwa take da dogon hannu, kuma take amfani da shi.

------------------------------------------------------------



Wata rana Kunkuru zai he ƙauyensu ziyara.

Yana cikin tafiya sai ya tsuntsaye guda biyu sun so wucewa ta saka.

Sai Kunkurun ya ɗaga kansa Sama ya ce, "Sannunku tsuntsaye, ko za ku rage min hanya? Domin Na gaji da tafiya wallahi."

Sai tsuntsaye suka sauko suka ce da Kunkuru, "Ai ba za mu iya tafiya da kai ba, kai ba ka da fuka-fukai."

Sai Kunkurun ya ce, "Ina da wata dabara, ku nemo Kara, ku kama gefe da gefe, no Kuma in hau tsakiya in riƙe Karan da baki na."

Sai tsuntsaye suka ce, "Mun yedda, Amma dole Sai ka yi shiriu da baking ka, domin in ka yi magana, za ka faɗo ƙasa."

Sai Kunkurun ya ce ya yarda, sai suka gwada dabarar sa.

Suna cikin tafiya a sama Sai suka so wucewa ta Saman kasuwa. Sai mutane suka ce, "Yau ga abin mamaki, tsuntsaye sun dauki Kunkuru."

So kuwa da kunkuru ya buɗe baki ya ce, "To ina ruwanku? Ku mutane kun cika Ido."

Kafin ya rufe bakinsa sai timmm... Kunkuru ya faɗo ƙasa. Bakin sa ya fashe, kokokon bayan sa ma ya farfashe.

Sai tsuntsaye suka ce, "So Dama sai da muka yi Maia kashedi, domin kuwa, Mun san halinka, ba ka yin shiriu da bakin ka."

------------------------------------------------------------



Mallam Ilu yana zaune  a ƙauyenmu kuma yana da kyanwa mai suna Safi.

Idan Malam Ilu ya tafi aiki, yakan bar ƙofa a buɗe.

Safi takan zauna a bakin kofa tana kula da gidan.

Idan karen maƙwabtansu ya matso kusa, Safi takan yi masa barazana.

Karen ya kan gudu.

Idan wani baƙo ya ƙwanƙwasa ƙofa, safi takan kai yakushi.

Baƙi sukan juya, su ruga a guje.

Idan Safi tana jin yunwa, ta kan rufe ƙofa.

Sai ta ci abincinta.

Daga nan Safi sai tayi tsalle ta haye doguwar kujera, ta yi barci har da minshari. Kurr! Kurr! Kur!

Idan Malam Ilu ya dawo, Safi sai ta miƙe cikin farin ciki tana yi masa maraba.

Malam Ilu da Safi sukan zauna, kowannensu yana karanta jarida.

------------------------------------------------------------



Tafin kafa

Kafa

Gwiwa

Kugu

Ciki

Kirji

Tafin hannu

Hannu

Gwiwar hannu

Kai

------------------------------------------------------------



Kombe da Juma sun kasance makota talakawa.
  
 Suna yin komai a tare da kansu.

Sai suka yi tunanin su sayi jaki.
  
Domin ya dinga daukar musu kaya.

Kombe ya kawo shawara, "Mu hada kudi mu sayi jaki."
  
Suka yi farin ciki.

Ana haka, sai baban Kombe ya mutu. Kombe ya samu dukiya mai yawa.
  
Nan da nan sai ya manta da abokinsa Juma.

Kombe yana son ya yanka jakinsu, ya ba karnukansa nama.
  
Juma yana bukatar jakin wajen yin aiki.

Sai suka je wajen Alkali. Shi kuma ya ce, "Sai s raba jakin gida biyu, kowannenku ya dauki rabi."

Sai Kombe ya kashe jakin.
  
Juma ya koma daukar kaya da kansa.

Daga nan sai Kombe ya fara tunanin kona bukkarsa, ya gina sabuwa.

Juma ya ce, "Nima tawa za ta kone, idan ka kona taka."
  
 Amma sai alkali ya sake ba Kombe nasara.

Bukkar Juma ta kone kurmus.
  
Alkali kuwa ya ce, "Ai Kombe iya bukkarsa kawai ya kona."

Juma ya dawo ba shi da gida kuma ba shi da jaki, dan haka yake kwana karkashin bishiya shi da iyalansa.

Juma ya yi aiki sosai a gona.

Shukar wakensa ta yi kyau matuka.

Sai yaran Kombe suka je suka ci wake mai yawa a gonar Juma.

Yaran suka ce da Juma, "Ka je ka tambayi babanmu domin ya biya ka kudin wakenka."

Juma ya je wajen Kombe, ya ce masa, "Ni bana son kudinka, wakena kawai nake so."

Sai alkali ya ce da juma, "Ka je ka yanka yaran sannan ka debi wakenka."

Juma ya ki sauraron Kombe.

Kombe ya dinga rokonsa, "Ka bari manya su shiga maganar."

Sai dattawan suka ce da Kombe, "Ka kashe masa jakinsa. Kuma ka kona bukkarsa."

Sai suka ce da Juma, "Kai kuma kashe yaran kombe ba abu ne mai kyau ba."

Kombe ya bawa Juma rabin dukiyarsa.
  
Daga nan suka zauna cikin farinciki.

------------------------------------------------------------



Ni mazamnin garin Daƙoro ne, wurin hamada ce,  akwai zafi ƙwarai, da itatuwa masu ƙaya, awakin garin sun fi mutanen yawa.

Kasuwa garin ma shiru ne, sai ƴan rumfuna. Ma fi yawan mutanen saman keke suke tafiya.

Wata rana, mahaifiyata ta kiranyo ni, ta ce mini, "Sani yau ka cika shekaru shidda. Za mu ba ka wani albishir."

"Mine? Mine?" na matsu in sani. "Gobe, za mu tafi kasuwar A-ci-da-kofato cikin mota," in ji ita, "Za mu tafi tare da kai!" 

Farkon tafiyata maraya! Na kwana ina jin daɗi, ban yi barci ba don murna.

Washe-gari, a tashar Daƙoro, na riƙe hannun mamata da na tantita ina sanye da sabbin kaya.

Ga ni nan ɗan ƙarami tsakanin mamata doguwa ramamma da tantita mai jiki.

Motar ta cika kuma ni ina zamne saman gwiwar mamata.

Zafi da gajiya kuma da murna sun sanya na yi barci tsawon bulaguron kuma ban yi kallo ba.

Rana ta yi sosai ko da muka iso kasuwar A-ci-da-ƙofato. A bakin kasuwar akwai wata mata tana saida hatsi.

Gaban kaɗan, wani mutum yana shirin fara saida dankali. Cikin wani lungu, akwai wata ƙaramar mata, da take ɗauke da wani jirgi na roba bula da yake ta haskawa.

Jirgin na wasan yara ne. "Mamma, dubi wannan jirgin." Amma ta ja ni ta hannu, muka tafi gaba.

A tsakiyar kasuwar, akwai wata babbar rumfa da ɗiyan itace iri-iri. Wasu na san su wasu ko ban taɓa ganinsu ba.

"Mi sunan wa'ƴannan ɗiyan itacen?" na tambayi mamata. Tana gwada mini kuma tana faɗa mini: "Lemun zaƙi ne da gwaiba." Na juya na ce,  "Wa'ƴannan fa?"

Duk cikin ƴaƴan itacen, na fi son tuffa. Ina son shi ƙwarai. Ina son in ji ɗanɗanonshi. 

Sai na ce ma mamata, "Kina iya saya mini guda?"

Ko da ta miƙo mini tuffar sai na sanya hannu biyu na karɓa, kuma na fara gurgurar wurin daɗin.

Ban taɓa jin daɗin ɗan icce kamar wannan. Shi kaɗai nake so.

Bayan na gama cin tuffar, sai na ɗaga kai sama don in ma mamata magana. Amma ban gan ta ba. Sai na dubi ta hanyar da muka zo, kuma ban gan ta, ban ga ba tantita. Na duba dama da hagun amma ban gan su ba.

"Ba ku ga mamata?" nake tamabayar mata masu saida dankalin turawa. Ba su ce mini komi ba. Sai na fara kuka.

Bayan ɗan lokaci, wata mata ta kama hannuna ta kuma kai ni wani wuri da ke akwai yara.

Wani mutum mai gemu da yawa ya tamabaye ni, "Mi sunanka yarona?"

"Sa-ni," na ce mishi cikin kuka.

Ina tambayar kaina, in yaran sun zo kasuwa ne suma. Sai na bar kuka don in ga ba wani yake cikin ɗaki yana sayan yaran.

Sai ga wata mata ta zo ta tafi da wani yaro. "Ni zan bi bayan shi," nake tunani. "Kenan ba ni ba komawa gida." Sai na fara kuka kuma.

Lokacin da na ji mutum mai gemu ya ce, "Ina Sani?" sai na ci gaba da kuka ƙwarai.

"Ban tafiya tare da ku!" ina kuka. Sai na ruga na kuje mishi.

Ko da mamata da tantita suka ji an kama sunana, sai suka rugo cikin ɗakin.

"Sani! Sani," ake kira da wata murya sananniya. Mamata ce.

Lokacin da na zabura in rungumi uwata sai tanti ta ce, "Sani mun yi ta neman ka don mu ba ka wata kyauta don ganin cikon shekarunka shidda."

Sai ta fiddo daga cikin jikarta wannan jirgin na roba na gani. "Naka ne," ta ce.

------------------------------------------------------------



A wani gari mai suna Magarya. Anyi wani mutum mai suna Bunu.

A garin Magarya, a kan zauna a yi ta hira da bada labarai masu ƙayatarwa

Da aka zo kan Bunu sai ya ce nasa labarin a kan damisa ne

Bunu ya gyara murya, ya fara cewa "Damisa kamar kyanwa ta ke".

Sai kowa ya ce "Lallai, haka ne".

Ya ce kuma "Tana da tsawon bindi".

Sai aka ce “Ummm, gaskiyar ka!

Lokacin da Bunu ya fahimci ya fara birge jama'a.

Sai ya yi farat ya ce "Ai lokacin da muke yara, malamin mu ya taɓa nuna mana damisa a bakin rafi."

Damisa, tana da ƙahon ta biyu masu tsawo kamar na barewa."

Sai kowa ya ƙyalƙyace da dariya ana yi masa ba'a.

"Ta tabbata Bunu baka san damisa ba!" Suna faɗi suna dariya.

Bunu ya ji takaici sosai.

Daga lokacin sai ya ce "Daga yau ba zan
sake ba da labarin abinda ban sani ba.

------------------------------------------------------------



A zamanin da can, dabbobi basu da kafafun tafiya. Dukan su jan ciki suke yi.

Mutane kaɗai keda ƙafafu, waɗan da Madugu ya basu.

Wata rana, Madugu ya ƙudurci bai wa kowace dabba ƙafafu. Ya sanar da su.

Dabbobin suka ce, "Yana da kyau sosai mu samu Ƙafafu." Suka yi rawa da waƙa.

Dabbobin suka ce, "Jan ciki yana yi masu wahala." Suna jin ciwo.

Da ranar ta zo, Dabbobin suka je gidan Madugu. Dabbobin sun jeru reras.

Ko wace dabba an bata ƙafafuwa huɗu. Tsuntsaye an basu ƙafafuwa biyu..

Komai ya canza bayan sun samu ƙafafu. Wasu rawa don murna. Wasu sun faɗi.

Sun je sun nuna wa mutane. Dabbobin suka ce, "Ba za mu ƙara jan ciki ba."

Ƙadandoniya ce ta zo daga ƙarshe.

Madugu ya ba ƙadandoniya dukkan ƙafafun da suka rage.

Ƙadandoniya cikin farin ciki sai ta ce, "Zan fi kowa ce Dabba sauri."

Bayan ƙadandoniya ta tafi, Maciji yazo yana roƙon Madugu ya bashi ƙafafu.

Madugu ya ce, "Na bayar da su duka." Maciji ya ce, "Nayi nauyin barci!"

Madugu ya duba ko akwai sauran ƙafafun, amma bai samu ragowar ko ɗaya ba.

Madugu ya ce, "Ƙa yi haƙuri." Maciji ya koma gida ransa ɓace.

------------------------------------------------------------



Mahaifina ya na son Fate-fate.

Ina son kanzon bature (cornflakes).

Mahaifina ya na son gahawa.

Ina son madara.

Mahaifina ya na son tuffa.

Ina son lemon-zaki.

Mahaifina ya na son Buredi. Ina son gasasshen Buredi.

Dukkan mu muna son Cin-cin.

------------------------------------------------------------

A ƙasar Kenya, a cikin wani ƙauye mai tsaunuka

da kwazazzabai, an yi wata yarinya mai taya

mahaifiyarta aiki a gona. Sunan yarinyar Wangari.

Wangari na sha'awar zama a waje, shi ya sa ta

shuka iri a lambun gidansu.

Lokacin da tafi son tafiya gida shi ne bayan faɗuwar

rana. Ta na bin kwararo don zuwa gida da kuma

kallon shuke-shuke.

Wangari yarinya ce mai ƙwazo da son zuwa

makaranta. Amma iyayenta sun fi son ta taya

su aikin gida. Da ta cika shekara bakwai sai

yayanta ya rinjayi iyayenta domin ta je makaranta.

Wangari ta yi murna matuƙa lokacin da aka

gayya ce ta zuwa Amurka ta yi karatu, sakamakon

ƙwazonta na son karatun littattafai.

A Jami'ar Amuruka ta koyi sababbin abubuwa da

yawa. Waɗanda suka haɗa da rayuwar tsirrai da

yadda suke girma. Sannan, da yadda suke

wasa da 'yan uwanta a ƙarƙashin inuwar

kyawawan bishiyoyin Kenya a daji.

Da zarar ta koyi wani abu ya kan ƙara mata ƙaunar

mutanen Kenya, tana son ganin su cikin farin ciki da

'yanci. Sannan, takan tuna Afirika a matsayin gida.

Yayin da ta kammala karatunta, sai ta dawo

gida. Amma, ƙasarta ta sauya. An sami manyan

gonaki a ƙasar. Mata ba su da itacen girki sannan,

jama'ar gari sun talauce, kuma yara suna fama da yunwa.

Wangari tayi tunanin abun yi. Ta koyawa mata

dabarun shuka irin itatuwa. Mata na sayar da

itatuwa da amfani da kuɗin domin kula da iyali.

Matan sun kasance cikin farin-ciki. Wangari ta

taimaka sun zama masu ƙwazo da matsayi.

Bayan lokaci mai tsawo bishiyoyin sun girma aka

fara samu gandun daji. Koguna suka fara gudana,

saƙonta ya fara mamaye Afirika. A yau miliyoyin

bishiyoyi sun samu a sakamakon gudunmuwar

irin da Wangari ta samar.

Mutanen duniya baki ɗaya sun yaba da ƙwazon

Wangari. Saboda haka ne, aka karrama ta da

shahararriyar kyautar nan ta zaman lafiya ta duniya

(NOVEL). Ita ce mace ta farko da ta fara samun

kyautar a Afirika.

Wangari ta rassu a shekara ta dubu biyu da

sha ɗaya (2011), amma mukan tuna ta duk lokacin

da muka ga kyawawan bishiyoyi.

------------------------------------------------------------

Kunkuru da kurege suna buƙatar kuɗi.

Sun ƙera farantai domin su kai kasuwa su sayar.

Kunkuru ya hango ana faɗa a kasuwa. Kunkuru da buddari ne suke

faɗa. Kunkuru yayi ƙara yace, "Kyale abokina."

Buddari ya ciji kunkuru a hanci.

Karyayyen hancin kunkuru ya kama ciwo.

Kunkuru ya samu karkataccen hanci saboda ya shiga faɗa.

------------------------------------------------------------

A wani kauye dake ɓangaren Mambilla Plateau a yankin Arewa

Maso-Kudu a Nijeriya, in ji wata yarinya mai suna Wanderimam wadda

ke taya mahaifiyarta aikin lambu. Wanderimam ta kance yarinyace

wadda bata sha'awar zaman gida. Ta yi amfani da wani irin tokobi wajen

tona kasa yayin datsa biciyoyi a cikin lambun iyayanta.

Wanderimam ta fi sha'war fauɗwar rana kan ko wani lockaci, yayin da ko

ina yayi duhu. Lokacin komawarta gida tana bin sakanin shuki da shuki

sannan ta haya kogi har ta karaso gida.

Wanderimam ta kasance yarinyace mai tsaninin dabara tun kamin

shigarta makaranta. Wannan dabaran na ta ya sanya iyayanta suka yanke

sha'awara kan su barta a gida ba sai ta yi karatu ba domin ta tayasu aikin

gida. Amma daga baya babban yayanta ya sanyanta a makeranta.

Ita yarinyace mai son karatu kullum, duk littafin da ta ci karo da shi sai ta

ga ta karance shi kaf. wani littafi da ta ci karo da shi. Wannan ya jawo mata

nasarar samun yin karatu a Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria.

Wanderimam ta yi matukar farin ciki domin ita yarinyace mai son sanin

abinda duniya ke ciki. A cikin Jamiar Ahmadu Bello dake

Zaria, Wanderimam ta kararci sababin abubuwa da dama. Inda take nazarin

fannin shuki da rayar da su. Wannen ya tunarta da ita yadde take wasa da

yayunta a cikin wani gandu dake Kurmi. Duk wani abun da ta karanta sabo sai

ya sanya ta kara son al'umar Jihar Taraba. Burinta a kullum shi ne ta ga

suna rayuwa cikin walwala. Duk abun da ta yi nazari, yana sanyata tuna

mahaifurta. Bayan kammalawar karatunta, Wanderimam ta dawo Jihar Taraba

inda ta tarar komi ya cenza ko kirare na hura wutar babu ga talauci da

yunwa ya mamaye ko ina, yara sun dawo Allah Sarki. Nan, Wanderimam ta yi tunanin

abunda ya kamata ta yi. Nan ne ta koyawa matan kauyen yadda za su yi

datsa biciyoyi da sirrai. Bayan wasu yan lokuta matan sun mori gajiyar

abinda suka shuka. Matan sun yi matukar farin ciki kwarai da irin

taimako masu da ta yi. Bayan wasu lokata, wanan biciyoyi da

suka datsa, ko suka datsa, sun zama gandu harma da samun koramai a

cikinta. Wannan abun da Wanderimam ta yi ya bazu a kasa baki

ɗaya a yanzu haka sama da biciyoyi miliyan suke raye daga iri na

Wanderimam. Daman an ce mai hakuri yaken dafa

dutse wataranan ya sha romonta. Duk ko ina a fadin kasan labarinta ya bazu

inda ta karba kyaututtuka da dama wanda hakan ya sauyata mace ta

farko a cikin kabilar Kuteb da ta karbi lamba ta yabo.

Wanderimam ta yi aure a shakara ta 2011. Duk lokacin da muka ga wata

biciya mai ban sha'awa, sai mun tuna da ita.

------------------------------------------------------------

Wahala na cikin ɓangaren rayuwar kowace halitta. Karnuka da ƙadangaru suma abin

halitta ne. Kare da Kadangare abokan juna ne na kusa. Suna tattaunawa a kan matsalar

rayuwa sai ƙadangare yace "Na sha walaha fiye da kai". Kare ya amsa masa 'Ba ka ga

yadda nake shan wahala ba lokacin neman abinci"?. Ƙadangare yace "Duk lokacin da zan

ci Ƙudaje sai su tashi sama, rayuwata tana ƙunci, ko da yake wani lokaci ina laɓewa a

jikin bango, saboda domin in samu sa'ar ƙudajen.

Suna cikin magana sai ga wasu mutane za su ci abinci, sai ƙadangare ya maƙale yana

kallon su. Shi kuwa kare ya matso kusa da su. Sai suka kore shi tare da duka, ya kuka

whoo! whoo!. Kare ya kasa gudu saboda yunwa, sai ya dawo saboda abincin. Sai aka

jefa masa abincin ɗankaɗan a fako mai tsananin datti. Ƙadangare yana maƙale a

kan bango ya na kallon duk abin da yake faruwa. Ƙadangare ya gyada kansa kaf!

kaf!kaf! yace "Lalle kare na shan wahala sosai.

Wanna shi ne dalilin da ya sanya duk inda ƙadangare ya ga kare ya ke girgiza kansa.

Shi ne ma ƙadangare ya fahimci cewa abinci wani gubar wani. Ka da ka kambama

matsalarka akan ta wasu,, za su iya zama sun fi ka matsala kuma su yi maka dariya.
